| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Kenya ta kama wata mata bisa zargin damfarar Ba’amurke dala 431,000 a yarjejeniyar cinikin zinare
‘Yansanda a Kenya sun kama wata mata da ake zargi da damfarar wani Ba’amurke dala 431,000 bayan ta yi masa ƙaryar cewa za ta iya samar masa da sandunan zinare na gaske masu nauyin kilo 400.
Kenya ta kama wata mata bisa zargin damfarar Ba’amurke dala 431,000 a yarjejeniyar cinikin zinare
Kenya ta kama wata mata bisa zargin damfarar Ba’amurke dala 431,000 a yarjejeniyar cinikin zinare / Reuters

‘Yansanda a Kenya sun kama wata mata da ake zargi da damfarar wani Ba’amurke dala 431,000 bayan ta yi masa alkawarin samar masa da sandunan zinare na gaske masu nauyin kilo 400.

Hukumar binciken manyan laifuka ta Kenya, Directorate of Criminal Investigations, ta bayyana a ranar Lahadi 17 ga Mayu, 2026 cewa an kama matar mai suna Mildred Kache, wadda aka fi sani da Sabreena Ayesha, a unguwar Kilimani da ke birnin Nairobi, babban birnin ƙasar.

Hukumar ta bayyana Kache a matsayin mace mai iya jan hankali da magana, tana mai cewa ita da wasu abokan haɗinta sun shawo kan Ba’amurken ne ta hanyar tabbatar masa cewa za su iya samar masa da kilo 400 na zinare a farashi mai rahusa fiye da na kasuwa.

Idan aka yi la'akari da sabon matsakaicin farashin zinare na kusan $145,000 a kowane kilo, to kilo 400 na wannan ma'adani zai kai aƙalla dala miliyan 58.

'An ja hankalinsa da tayi mai gwaɓi'

Ana zargin Kache da abokan haɗinta da bayar da tayin kilo 400 na zinare kan kuɗi sama da dala 431,000, wanda ya kai kusan kashi 7 cikin 100 ne kawai na ainihin darajar zinariyen a kasuwa.

Hukumar binciken manyan laifukan ta ce Ba’amurken ya amince da yarjejeniyar saboda ganin kamar dama ce ta samun riba mai yawa, lamarin da ya sa ya tafi birnin Nairobi domin kammala yarjejeniyar.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce:

“Komai ya bayyana tamkar gaskiya ne, domin an shirya takardu, an gudanar da tattaunawa, sannan bayan an rattaba hannu kan yarjejeniyar damfarar, wanda abin ya shafa ya tura miliyoyin kuɗi cikin asusun bankunan waɗanda ake zargin, yana tunanin za a isar masa da zinaren kamar yadda aka yi alkawari.”

Hukumar ta ƙara da cewa: “Shigar kuɗin asusun ke da wuya, sai waɗanda suka kira kansu masu cinikin zinarien suka yi ɓatan dabo tamkar ƙura a iska. Kiran waya ya daina shiga, kuma ba a isar da ko giram ɗaya na zinare ba.”

'An yaudare shi'

Hukumar binciken manyan laifuka ta ce Ba’amurken ya kai rahoton damfarar gare su ne bayan da ya fahimci cewa an yaudare shi.

Hukumar ta bayyana cewa binciken ƙwaƙwaf da tattara bayanan sirri ne ya kai jami’anta gidan Kache da ke unguwar Kilimani, inda aka kama ta, yayin da ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin suke tare da ita, amma wani Ibrahim Yusuf Mohamed ya tsere.

Hukumar ta ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike da shirye-shiryen gurfanar da Kache a kotu, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargin da hannu a lamarin.

Sashe na 313 na kundin dokokin laifuffuka na Kenya ya tanadi hukuncin daurin shekara uku ga duk wanda aka samu da laifin karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.

A baya bayan nan dai an samu ƙaruwar damfarar da ta shafi bogin cinikin zinare musamman a wasu ƙasashen Afirka da ba sa haƙo zinare, inda hukumomi ke gargadin jama’a su kasance cikin taka-tsantsan, musamman idan farashin da ake bayarwa ya yi matuƙar rahusa fiye da yadda ake tsammani.