| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 36 da aka sace a kasar, sun kuma halaka ’yanta’adda da dama
Sojojin sun ce sun halaka wasu manyan kwamandojin ’yanta’adda guda biyu tare da jikkata wani na uku yayin wani samame da suka kai kan wasu maɓoyar ’yanta’adda da ake zargi a Kogo da ke Matazu, Jihar Katsina, a ranar 31 ga Agusta
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 36 da aka sace a kasar, sun kuma halaka ’yanta’adda da dama
Sojojin Nijeriya a lokacin da suke gudanar da wani aiki a 'Yantumaki B da ke Jihar Katsina

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka ’yanta’adda da dama a sabbin ayyukan soji da suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.

Daraktan Ayyukan Yaɗa Labaran Sojoji, Manjo Janar Michael Onoja ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, kan ayyukan sojin da aka gudanar tsakanin 31 ga Agusta zuwa 3 ga Satumban, 2026.

Ya ce dakarun sun hallaka wani ɗanta’adda a ranar 1 ga Satumba, bayan da suka tarwatsa wani abin fashewa da aka dasa a kan babbar hanyar samar da kayayyaki ta Miyanti-Banki Junction a Bama, Jihar Borno.

A cewarsa, dakarun sun kwato bindiga, harsasai da kuma na’urar tayar da bam bayan wannan samamen.

Ya ce an kuma hallaka wani ɗanta’adda yayin wata arangama da aka yi a Lamusuri Crossing Point da ke Gujba, Jihar Yobe, inda aka kwato bindiga da harsasai.

Onoja ya ce dakarun sun kuma kama wani ɗanta’adda da ya tsere daga hannun ƙungiyar a kusa da Sabsawa, Bama, a ranar 31 ga Agusta, bayan ya tsere saboda yunwa da tsananin wahala.

Ya ce dakarun sun kama wani mutum a Konduga da ake zargi da safarar kayan abinci zuwa wani sansanin ’yanta’adda a Bama.

A cewarsa, dakarun sun kuma kama wani tsohon ɗanta’adda da ya koma mai ba da bayanan sirri a Damasak, Ƙaramar hukumar Mobbar, a ranar 1 ga Satumba.

Onoja ya ce mata da yara 21 sun miƙa wuya ga dakarun a Mafa da ke Dikwa, a ranar 2 ga Satumba, bayan ɓarkewar faɗa tsakanin ƙungiyoyin ’yanta’adda masu hamayya da juna.

Ya ƙara da cewa an kuma kama wani ɗanta’adda da ya tsere a kusa da gadar Amuda da ke Gwoza, yayin da aka kama wani da ake zargi ɗan leƙen asirin ’yanta’adda ne a kan hanyar Kauwa zuwa Kukawa.

Onoja ya ce dakarun Operation Fansan Yamma sun ci gaba da kai hare-haren soji kan ’yanta’adda da masu garkuwa da mutane a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara.

Ya ce dakarun sun halaka wasu manyan kwamandojin ’yanta’adda guda biyu tare da jikkata wani na uku yayin wani samame da suka kai kan wasu maɓoyar ’yanta’adda da ake zargi a Kogo da ke Matazu, Jihar Katsina, a ranar 31 ga Agusta

 

 

Rumbun Labarai
Nijeriya ta musanta zargin goyon bayan yunƙurin 'juyin mulki' a Nijar
Hukumar DSS ta Nijeriya ta ƙwato bindigogi 676 da harsasai 332,000
INEC za ta yi zaɓen gwaji na Shugaban Ƙasa gabannin zaɓen 2027 na Nijeriya
Ɓarayin daji sun ƙaƙaba harajin naira miliyan 40 kan mazauna wani gari a Sokoto
An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya - Hukumomi
Annobar da ake zargi mashaƙo ce ta kashe aƙalla mutum 23 a Jihar Filaton Nijeriya
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kashe ‘yanta'adda 1,500 da kubutar da mutane 777 a watanni biyu
EFCC ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya
Tinubu ya jinjina wa jami’an tsaron Nijeriya kan ceto masu yi wa kasa hidima da aka yi garkuwa da su
Gwamnatin Kano tana bukatar rigakafin cutar mashaƙo miliyan tara daga gwamnatin tarayya
Nijeriya ta nuna damuwa kan abin da ya faru a makwabciyarta Nijar
Shugaba Tinubu zai tafi Turai don fara hutun makonni uku
Babban Sufeton ‘Yansandan Nijeriya ya matsa ƙaimi don ceto waɗanda aka sace a masallacin Jihar Neja
'Yansandan Nijeriya sun kama likitoci kan zargin safarar mutane da cire musu ƙoda
Amurka na shirin janye sojojinta 200 da ta tura Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta gargaɗi al’ummomi 915 a jihohi 19 kan barazanar ambaliyar ruwa
Sufeta Janar na ’Yansandan Nijeriya ya tura AIG zuwa jihar Neja don ceto masallatan da aka sace
EFCC za ta ba da ladan kashi 5 cikin 100 ga wanda ya ba da bayanai kan kadarorin sata da ke ƙetare
Hedikwatar tsaron Nijeriya ta tattauna da jakadan Saudiyya kan ƙarfafa alaƙar tsaro
Masu garkuwa da mutane a Nijeriya sun tara naira biliyan 7 na kuɗin fansa: Bincike