Daga tsaro zuwa kasuwanci: Abin da ya sa juyawar Nijeriya zuwa Turkiyya ke da muhimmanci

Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa Turkiyya ta nuna muhimmancin Turkiyya a matsayin abokiyar hulɗa a Afirka da kuma zamanta wani ƙarfi na daidaita tsaron nahiyar, in ji masana.

By
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya tarbi Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Ankara, Turkiyya. / AA

Ganawa tsakanin Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya da Bola Tinubu na Nijeriya ya nuna sauyi a yadda Nijeriya ke tsara dangantakarta da Turkiyya, wanda za a iya taƙaita shi da layi ɗaya: “Mai amfani kuma mai hangen nesa”.

Wannan shi ne saƙon Shugaba Tinubu ga 'yan Nijeriya a ƙarshen ganawarsa da mai masaukin baki a Ankara, inda ƙasashen biyu suka sanya hannu kan yarjejeniyoyi guda tara a fannoni kamar tsaro, kasuwanci, ilimi, manufofin 'yan ƙasa a kasashen waje da bunkasar zamantakewa.

Ga Nijeriya, wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na faɗaɗa haɗin gwiwar waje da abokan hulɗarta na gargajiya, yayin da take fuskantar matsalar tattalin arziki da ke farfadowa da kuma matsalar tsaro mai sarƙaƙiya. Shugaba Tinubu ya ce ƙasar a “buɗe take ga kasuwanci ba tare da shinge ba, buɗe ga ra'ayoyi, ƙwarewa, da zuba jari da ke samar da fa’ida da wadata”.

Haka kuma ziyarar ta nuna karuwar kasancewar Turkiyya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa a Afirka da kuma zama wani abu mai ƙarfi wurin daidaita tsarin tsaron nahiyar, kamar yadda masana suka shaida wa TRT Afrika.

Ministan Tsaro na Nijeriya Christopher Musa ya shaida wa TRT Afrika cewa yarjejeniyoyin soja da aka sanya wa hannu yayin ziyarar za ta bai wa Turkiyya damar mika fasaha wajen kera kayan soja. Ya ƙara da cewa wasu kamfanonin Nijeriya sun riga sun fara tattaunawa da kamfanonin tsaron Turkiyya kan yiwuwar haɗin gwiwa wajen ƙera kayayyaki tare.

“Mu ƙasa ce mai ƙarfi a yankin. Idan muka fara kera wannan, za mu iya taimaka wa ƙasashen makwabta su samu shi ma. Ayyukan yi za su ƙaru, kudaden musayar waje za su shigo. Don haka zai zama riba ga ƙasashen biyu kuma wannan ne muke so,” in ji ministan.

“Kuma shugaban Turkiyya a koyaushe yana goyon bayan Nijeriya kuma muna matuƙar godiya gare shi da gwamnatin Turkiyya, za mu ci gaba da yin aiki tare,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Kasar ta Yammacin Afirka tana fama da ƙungiyoyin ta'addanci kamar Boko Haram da ISWAP waɗanda suka nemi samun matsayi a yankin arewa maso gabashin kasar. Har ila yau, ana ci gaba da samun arangama tsakanin manoma da makiyaya, da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa da kungiyoyin da ke ɗauke da makamai ke aiwatarwa.

Amma Nijeriya na fuskantar matsaloli saboda rashin dogaro a kan ƙwarewar ƙera kayan tsaro.

Masana sun ce yarjejeniyar ta tsaro ita ce mafi muhimmanci daga ziyarar Shugaba Tinubu.

“Wannan ziyarar na iya zama kamar ziyara ta diflomasiyya ta al'ada, amma akwai wata babbar manufa a bayan ta. Turkiyya ba wai tana magana ne kawai da Nijeriya ba, amma tana bayar da sabuwar babbar dama ga sauran yankin Afirka. Harkar ita ce gina haɗin gwiwa ta dabaru wadda za ta iya nuna makomar nahiyar,” in ji Göktuğ Çalışkan, ƙwararren masani kan hulɗar ƙasa da ƙasa a ANKASAM, wata cibiyar tunani ta Turkiyya.

Bugu da ƙari, kwarewar Turkiyya da nasarorinta a yaki da ta'addanci ana ganin za su samar da muhimmiyar taswira ga ayyukan yaki da ta'addanci na Nijeriya.

“Turkiyya na iya yin haɗin gwiwa da rundunar ƙasa da ta sama ta Nijeriya ta hanyar bayar da jagoranci a fannoni kamar jiragen sama marasa matuƙa (UAVs), helikofta, gyara da kanikanci, shirye‑shiryen horo na soja na zamani, da ƙwarewar yaki da ta'addanci. Wannan na iya ƙara ƙarfafa damar Nijeriya a yaki da ta'addanci da inganta tasirin ayyukanta a fagen,” in ji Kenan Toprak, mai bincike kan harkokin Nijeriya.

A bangaren tattalin arziki, kasashen biyu sun kafa kwamiti haɗin gwiwar tattalin arziki da nufin karfafa hulɗar kasuwanci. Shugabannin sun sanya manufa ta ƙara yawan ciniki tsakanin Nijeriya da Turkiyya zuwa dalar Amurka biliyan 5.

Nijeriya ta zama babbar abokiyar cinikayyar Turkiyya a yankin Afirka a 2025 idan aka haɗa fitar da mai, in ji ma'aikatar kasuwanci ta Turkiyya.

“Turkiyya na ba Nijeriya manyan damammaki na kasuwanci a fannoni da dama ciki har da ababen more rayuwa da gine‑gine, makamashin da za a sabunta, fasaha, noma da abinci, masana'antar sauƙi da kayayyakin amfani, tsaro da soja, da yawon bude ido da hadin kan al'adu,” in ji Toprak.

Ya ƙara da cewa: “Kwarewar Turkiyya a manyan ayyukan ababen more rayuwa na ba da damar haɗin gwiwa da ta dace da hangen nesa na Nijeriya na sabunta tsarin gine‑gine da tattalin arzikinta. Yayin da bambancin kasuwanci ke ƙaruwa, damar kamfanonin Turkiyya na zuba jari a Nijeriya za su ƙaru kuma damar samar da ayyukan yi za su faɗaɗa a Nijeriya.”

Kuma yayin da hulɗar kasuwanci da ta soja ke ƙaruwa, haka ma alaƙar zamantakewa za ta bunƙasa, tare da yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu a fannin kafofin watsa labarai da sadarwa, ilimi mafi girma, horon diflomasiyya, da batutuwan zamantakewa da na mata. Manufar ita ce sauya yadda mutane daga ƙasashen biyu ke kallon juna, in ji masana.

“Yarjejeniyar kafofin watsa labarai musamman tana da muhimmanci a nan ma. Tsawon shekaru, Afirka mafi yawa tana bayyana a labaran duniya ta fuskar rikice‑rikice, juyin mulki ko masifu. Haɗa tsarin watsa labarai tsakanin Turkiyya da Nijeriya wani yunƙuri ne na karya irin waɗannan labaran masu fuska ɗaya. Horon aikin jarida na haɗaka, musayar labarai da ganin fuskokin juna a talabijin za su iya ƙara muryar Nijeriya da ƙara hangen Turkiyya a yadda ake magana game da Afirka,” in ji Çalışkan ga TRT Afrika.

“Ba za a tuna Turkiyya a Afirka kawai saboda kayan soja da take sayarwa ba. Za a danganta ta da labarin da ta rubuta tare da abokan hulɗarta na Afirka, kuma Nijeriya na daga cikin manyan marubutan haɗin gwiwa na wannan labarin,” in ji Çalışkan.