A ranar Alhamis din nan, Turkiyya ta kira haramtaccen matakin Isra'ila kan jirgin ruwan agaji da ke zuwa Gaza da nufin kai agajin gaggawa "fashin teku," tana mai cewa tana daukar "dukkan matakan da suka wajaba" game da 'yan kasarta da sauran fasinjojin da ke cikin jirgin.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce, "Ta hanyar kai hari kan jirgin ruwan Global Sumud, wanda ke neman jawo hankali kan bala'in jinkai da mutanen Gaza da ake zalunta ke fuskanta, Isra'ila ta kai hari kan darajojin jinkai da dokokin kasa da kasa."
Ta ce ayyukan Isra'ila sun kuma karya dokar 'yancin zirga-zirga a cikin ruwan kasashen duniya, ta kara da cewa: "Muna kira ga kasashen duniya da su dauki matakin hadin gwiwa kan wannan mummunan aiki da Isra'ila ta aikata."
"Ana daukar dukkan matakan da suka wajaba tare da hadin gwiwa da kasashen da abin ya shafa game da halin da 'yan kasarmu da sauran fasinjojin da ke cikin jirgin ke ciki," in ji Ma’aikatar.
Jirgin ruwan da ke zuwa Gaza a safiyar Alhamis din nan ya bayyana cewa sojojin ruwan Isra'ila sun nakasa injinansu kuma sun lalata taswirar hanyar jirgin yayin da aka kuma kama su, lamarin da ya sa daruruwan mutane suka shiga taskua.
Kungiyar da ta shirya taron Global Sumud Flotilla ta ce jiragen ruwan sojin Isra'ila sun kewaye ayarin a cikin ruwan ƙasashen duniya kusa da tsibirin Crete na Girka, inda suka toshe hanyoyin sadarwa da kuma katse hulɗa da jiragen ruwa 11.
Jirgin na dauke da fararen hula 400 da ke da manufar bude hanyar jirgin ruwa ta kai agaji Gaza da Isra'ila ta toshe tun shekarar 2007.
Yaƙin kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza, wanda ya fara a watan Oktoban 2023, ya ƙara ta'azzara yanayin yankin, inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 72,600 tare da raunata sama da 172,400, kuma ya haifar da barna mai yawa wanda ta shafi kusan kashi 90 cikin 100 na kayayyakin more rayuwa na fararen hula.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tun daga watan Oktoban 2025, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Gaza kuma ta takaita shigar da kayan agaji cikin yankin.


















