| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
UEFA ta sha alwashin ƙaurace wa FIFA idan aka ci gaba da shirin sayar da Gasar Kofin Duniya
'Babu tawagar ƙwallon ƙafar hukumar ƙwallon ƙafar Turai UEFA da za ta shiga ko wace gasar FIFA idan har wannan shirin ya ci gaba da kasancewa,' in ji hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai
UEFA ta sha alwashin ƙaurace wa FIFA idan aka ci gaba da shirin sayar da Gasar Kofin Duniya
UEFA ta sha alwashin ƙaurace wa FIFA idan aka ci gaba da shirin sayar da Gasar Kofin Duniya

Dukkan hukumomin ƙwallon ƙafa na Turai (UEFA) 55 sun haɗa kai wajen goyon bayan ƙaurace wa duk wata gasar FIFA idan Hukumar Ƙwallon Ƙafar ta Duniya ta ci gaba da shirin sayar da hannayen jari wasu daga cikin jerin gasarta ga ƙungiyoyi masu zaman kansu, in ji wata sanarwar da aka fitar bayan wani zama na gaggawa ranar Alhamis.

UEFA ta ce mambobin ƙungiyar “sun tsaya wuri ɗaya” kuma sun “sun haɗa baki ba tare da tababa ba ” wajen yin watsi da shawarar FIFA ta mayar da mallakar Gasar Kofin Duniya ta FIFA da ma sauran gasar hukumar zuwa ga ‘yan kasuwa.

“Sakamakon tattaunawar yau, babu wata tawagar ƙwallon ƙafa ta wata ƙasar UEFA da za ta shiga ko wace gasa ta FIFA idan har waɗannnan shawarwarin suka ci gaba, sai dai idan an an yi fatali da wannan shawarar gabaɗaya da kuma samun tabbaci daga FIFA cewa ba za ta sake buɗe jagorancinta ko gasarta ga ikon ‘yan kasuwa ba,” in ji sanarwar.

“Ba za a iya yi wa Gasar Kofin Duniya kamar wata hajar zuba jari ba. Ɗaya ce daga cikin manyan ababen tarihi na ƙwallon ƙafa ...Babu wani ɓangarenta da ya kamata a sallamar wa ‘yan kasuwa. Gasar Kofin Duniya ba ta sayarwa ba ce,” a cewar UEFA.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai ɗin ta kuma soki yadda hukumar FIFA ta ɗauki shawarar, tana mai cewa “a asirce aka shirya shawarar kuma aka zo daf da amincewa da ita ba tare da tuntuɓa mai ma’ana ba ” da masu ruwa da tsaki na ƙwallon ƙafa.

“Wannan ba kawai babbar gazawar shugabanci ba ce, amman ƙaurace wa nauyin da ya ratayu a kan hukumar FIFA a matsayinta ta jagorar harkar ƙwallon ƙafa ta duniya,” kamar yadda ta faɗa.

Zaman na gaggawa ya biyo bayan ƙarin adawa ga shawarar da shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA Gianni Infantino ya gabatar ta kafa kamfanin kasuwanci na FIFA (FFE), wani ƙaramin kamfani da zai kula da Gasar Kofin Duniya da sauran harkokin kasuwanci.

Da farkon wannan makon, FIFA ta ce da yawa daga cikin hannayen jarin kamfanin FFE da kuma ƙarfin faɗa-a-jiza su kasance na FIFA ne, inda masu zuba jari daga waje za su riƙe kaɗan daga cikin hannayen jarin kuma su kasance ba su da ƙarfin faɗa-a-ji wajen jagorancin ƙwallon ƙafa ko kuma yanke hukunci kan wasanni.

Hukumar Ƙwallon Ƙafar ta ce shawarar za ta ƙara kuɗaɗen haɓaka harkokin mambobin hukumar 211, kuma hakan zai ci gaba ne kawai idan da yawa daga cikinsu suka yarda da shawarar.

Rumbun Labarai
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Habasha ta shiga takarar ɗaukar nauyin gasar AFCON ta 2028
An sayar da ƙwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a kan $3.35M
Ɗan Nijeriya Semi Ajayi ya taimaka wajen yi wa Man Utd dukan wulaƙanci a farkon Gasar Firimiya
Cristiano Ronaldo ya fara kakarsa ta 25 da ƙwallonsa na 977 a tarihin wasansa
EFCC ta fara binciken Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF
Jamal Musiala na Bayern Munich ya ce farfaɗiyar sandarewa ce ke damun sa
Patrick Vieira, tsohon ɗanwasan Arsenal ya zama sabon kocin tawagar Senegal
Kamaru ta lashe Kofin WAFCON a karon farko bayan ta doke Malawi
Lionel Messi ya ɓarar da fenareti na uku a jere yayin da aka lallasa kulob ɗinsa da ci 4-1
Ɗanwasan Sifaniya da ya ci Gasar Kofin Duniya Ferran Torres ya koma PSG daga Barcelona
Hukumomin ƙwallon ƙafa 6 na Larabawa, ciki har da Qatar da Morocco na goyon bayan Infantino na FIFA
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi FIFA a kan maye gurbin Infantino
Manyan hukumomin ƙwallon ƙafa na zargin shugabancin FIFA da ‘cin amana’
Mohamed Salah ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu da Trabzonspor ta Turkiyya
Danwasan Chelsea, Mudryk, ya dawo kwallo bayan dakatarwar kwana 600 bisa laifin shan kwayoyin kuzari
Arsene Wenger ‘ba shi da masaniya’ kan shirin Infantino na sayar da hannun-jarin Gasar Kofin Duniya
FIFA ta gaza hukunta Isra'ila kan karya dokokinta, a cewar hukumar Kwallon Kafa ta Falasɗinu
Masu adawa da Infantino sun yi barazanar gudanar da gasar kofin duniya ba a karkashin FIFA ba