Ƙasar Turkiyya ta ƙaddamar da sabbin ƙa'idoji kan kafafen sada zumunta da nufin ƙarfafa kariya ga yara da matasa masu amfani da intanet.
Turkiyya ta bi saun ƙasashe irin su Australia da Faransa wajen ɗaukar irin waɗannan matakai, inda ƙa'idojin suka mayar da hankali kan inganta tsaro, daƙile lalatattun bayani, da kuma tabbatar da ɗaukar mataki cikin sauri kan abubuwan da ke da cutarwa.
A ƙarƙashin sabbin dokokin, yara ‘yan ƙasa da shekara 15 ba za su iya buɗe asusun sada zumunta ba, kuma an wajabta wa kamfanoni su samar da tsarin tantance shekaru mai inganci. Su ma ga matasa daga shekara 15 zuwa sama, dole ne kamfanonin su samar musu da tsari na daban wanda ya dace da shekarunsu.
Matakan Tabbatar Da Dokar Mataki-Mataki
Waɗannan ƙa'idoji sun samar da ƙarin damar kula da yara ga iyaye, inda aka buƙaci samar da na'urori ko manhajoji da za su ba iyaye damar sarrafa asusun yaransu da kuma taƙaita lokacin da suke ɗauka a kan intanet.
Haka kuma, dole ne kamfanonin sada zumunta su ɗauki matakan hana tallace-tallace na yaudara da kuma rage haɗarin da ke tattare da intanet. A yanayin da ya shafi tsaron ƙasa, dole ne manyan kafafen sada zumunta su cire duk wani bayani da aka umarce su su cire a cikin sa'a ɗaya kacal.
Manyan ƙa'idoji za su shafi kafafen masu mutum sama da miliyan 10 a kowace rana a Turkiyya.
Domin hana maimaita kura-kurai, za a tilasta wa kamfanonin amfani da kirkirarriyar basira (Artificial Intelligence) don tabbatar da cewa duk bayanan da aka taɓa cirewa ba a sake ɗora su ba.
Hukumomi sun shimfiɗa matakan hukunci kamar haka:
Idan kafa ta ƙi bin doka, za a hana ta karɓar sabbin tallace-tallace.
Idan hakan ya ci gaba, hukuma za ta iya neman izinin kotu don rage saurin intanet na wannan kafa da kashi 50 cikin ɗari, sannan har kashi 90 cikin ɗari idan har ba su gyara ba.
Dokokin sun haɗa har da kafafen wasannin intanet (gaming platforms), inda aka hana wasannin da ba su da rukunin shekaru da suka dace. Kamfanonin wasanni na ƙasashen waje masu mutum sama da 100,000 a kowace rana, dole ne su naɗa wakilin shari'a a cikin ƙasar Turkiyya.
Wannan doka na nufin samar da yanayin intanet mai aminci da kuma bayyana gaskiya, kuma za su fara aiki ne watanni shida bayan wallafa ka’idojin.















