Jamus ta soki yaƙin Isra'ila da Amurka kan Iran, ta ce 'babu dabarar ficewa'
Ministan Tsaro Boris Pistorius ya yi gargaɗin cewa yaƙin da Isra'ila da Amurka ke yi a kan Iran zai yi tasiri kan tattalin arzikIn duniya kuma ya jaddada buƙatar da ke akwai ta amfani da diflomasiyya.
Ministan Tsaron Jamus Boris Pistorius ya soki yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kan Iran da kakkausar murya ranar Alhamis, yana mai cewa rikicin ba shi da wata dabara bayyananniya.
“Abin da ya fi damu na game da wannan yaƙin shi ne babu tuntuɓa, babu dabara, babu bayyananniyar manufa kuma abu mafi muni a fahimtata shi ne babu dabarar ficewa,” kamar yadda ya shaida wa wani taron manema labarai tare da takwaransa na ƙasar Australia Richard Marles a birnin Canberra, na Australia.
“Wannan yaƙin bala’i ne ga tattalin arzikin ƙasashen duniya. Sakamakonsa a bayyane yake bayan sama da mako biyu kawai. Ba a tuntuɓe mu ba kafin yaƙin. Ba yaƙinmu ba ne. Kuma shi ya sa ba ma son a ja mu cikin wannan yaƙin — idan zan faɗa muku gaskiya,” in ji shi.
Pistorius ya jaddada cewa ana buƙatar wata mafita ta diflomasiyya “nan ba da jimawa ba.”
Ya yi garɗin cewa rashin zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya zai shafi duk duniya.
“Kuma shi ya sa muke a shirye domin tabbatar da kowane irin zaman lafiya. Idan muka cim ma tsagaita wuta, za mu tattauna kowane mataki na tabbatar da zaman lafiya, musamman domin tabbatar da kaiwa da komowa ta hanyar ruwa a mashigin Hormuz.”
Tattaunawar Amurka da Iran
A Ranar Laraba Jamus ta ce lokaci ya yi da za a matsa kaimi wajen amfani da diflomasiyya domin kawo ƙarshen yakin da ake yi a Iran.
“Ina ganin muna wani mataki da za mu tattauna da gaske. Dole mu jira mu ga sakamakon tattaunawar (Iran da Amurka ta) Pakistan – tattaunawar da ba ma ciki, amma ga dukkan alamu ana yinta, kuma mun yi maraba da ita,” kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Jamus Johann Wadephul ya shaida wa wani taron manema labarai a Berlin tare da takwaransa na Tunisia Mohamed Ali Nafti.
Hare-haren sun yi ƙamari tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare ta sama kan Iran ranar 28 ga watan Fabarairu, inda Tehran ke mayar da martani da hare-haren jirage mara matuƙa da na makamai masu linzami a kan Isra’ila da ƙasashen Larabawa dake Gaɓar Teku waɗanda suka karɓi baƙuncin kayayyakin sojin Amurka.