Yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya take taimakawa wajen rage tunzurin yanki ta bayan fage
Gwamnati a Ankara tana amfani da diflomasiyar bayanan asiri don buɗe ƙofofi da hana ƙazancewar rikici, da kuma taimakawa tsagaita wuta, kamar yadda majiyoyin tsaro na Turkiyya suka faɗa.
Hukumar Bayanan Sirri ta Turkiyya (MIT), ta kasance tana aiki a bayan fage don taimakawa rage tashin hankali tsakanin Amurka da Iran, in ji wasu majiyoyin tsaro na Turkiyya, inda suke nuna ƙaruwar rawar da Ankara ke takawa a matsayin mai daidaita lamuran yankin.
Majiyoyin sun ce, MIT ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da cibiyoyi daban-daban na gwamnati ƙarƙashin umarnin fadar shugaban ƙasa, don sauƙaƙa yiwuwar tsagaita wuta da hana tsananta rikicin.
Kafin rikici ya ƙara tsananta, hukumar ta shiga mu’amaloli na diflomasiyya masu zurfi da duk ɓangarorin don hana ɓarkewar yaƙi. Da zarar an soma tashin hankali, MIT takan yi amfani da ikonta na musamman wajen sadarwa da ɓangarori biyu, tana ci gaba da buɗe hanyoyin tattaunawa tsakanin ɓangarorin da ke yaki.
Jami’an Turkiyya sun ce hukumar leƙen asirin ta mayar da hankali kan muhimman abubuwa da dama, ciki har da hana rikicin yaɗuwa a faɗin yanki, da rage rashin fahimta tsakanin masu rikicin, da isar da saƙonnin da ke nufin rage tashin hankali.
MIT tana kuma yin aiki wajen gano hanyoyin da za su iya dakatar da yaƙi, tana amfani da dangantakarta da ta kafa a birane da dama na manyan ƙasashe.
Baya ga manyan ɓangarorin da abin ya shafa, hukumar ta yi tattaunawa da ƙasashe kama daga Iraki, Pakistan, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Saudiyya, Kuwait, Masar, Birtaniya, Jamus, Faransa da Italiya, abin da ke jaddada matsayin Turkiyya a tsarin tsaro na yankin.
Majiyoyi sun ƙara da cewa, MIT ta ci gaba da kusantar juna da abokan aikinta na Iran, ciki har da jami’an da ke da alaƙa da Rundunar Juyin Juya Hali (IRGC), tana mai miƙa shawarwari da saƙonni da nufin kawo ƙarshen husuma.
Baya ga ƙoƙarin shiga tsakani, hukumar ta kuma tallafa wajen ayyukan ceton mutane, da haɗin gwiwar jinƙai daga wuraren da rikici ya shafa, abin da ke nuna irin tsarin martanin Ankara ga rikice-rikice.
Jami’an Turkiyya sun ƙara cewa, MIT ta ɗauki matakai don tabbatar da cewa rashin tabbas a Iran bai haifar da tashin hankalin ƙabilanci ba ko ya raunana manufofin tsaron cikin gida na Turkiyya.