Masana da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun bayyana cewa Isra'ila ta ƙirƙiri yunwa a Gaza ta hanyar manufofin yunwatarwa, inda kowane mataki ke ƙara tsananta kankanewa kan abinci, har sai da yunwa ta zama ba makawa.
A ƙarshen watan Agusta, Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta sanar a hukumance cewa akwai yunwa a Gaza, kuma ta tabbatar da abin da wasu ƙungiyoyi masu sa-ido da masana suka daɗe suna faɗa tsawon watanni.
Wata guda bayan haka, wani kwamiti mai zaman kansa na bincike na MDD ya tabbatar cewa Isra'ila ta aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.
Bayan haka, manyan jami'an jin-ƙai kamar shugaban agaji na MDD, Tom Fletcher, sun yi kira mai tsanani da jaddadawa kan a kawo ƙarshen “hana kayan buƙata da taimako” da Isra'ila ke yi — abin da Firaminista Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa suka ƙi amincewa da shi.
Ga Ramy Abdu, shugaban ƙungiyar Euro-Med Human Rights Monitor da ke Geneva, wannan manufa ta hana abubuwan buƙata na rayuwa tana tabbatar da niyyar Isra'ila na jefa Gaza cikin yunwa da kashe Falasdinawa da yawa.
“Yunwar Gaza ta bambanta da sauran saboda ba sakamakon bala'i ko rugujewar tattalin arziƙi kaɗai ba ne,” Abdu ya faɗa wa Anadolu. “Maimakon haka, wata manufa ce ta amfani da abinci da ruwa a matsayin makamai na yaƙi da kisan ƙare-dangi.”
Ya jaddada cewa jami'an Isra'ila sun bayyana wannan niyya tun farkon yaƙin.
“A ƙarƙashin dokar jin-ƙai ta ƙasa-da-ƙasa, amfani da yunwa a matsayin makami kan fararen hula laifi ne na yaƙi, amma a Gaza, ana aiwatar da wannan laifi a fili kuma a bayyane,” in ji shi.
‘Raunin da aka haddasa’ ya haifar da ‘kisan mummuƙe’
Isra'ila ta ci gaba da lalata tsarin wadatar abinci a Gaza tun kafin watan Oktoban 2023. Ta kafa takunkumi a shekarar 2006 wanda ya bai wa hukumomin Isra'ila iko kan dukkan iyakokin shiga da fita, har ma a wasu lokuta suna lissafa adadin kuzarin da ake yarda wa kowane Bafalasɗine ya ci a rana.
Daga shekarar 2023, mutane huɗu cikin biyar a Gaza suna dogaro da taimako, rashin aikin-yi a tsakanin matasa ya kai kashi 67 cikin 100, kuma cututtuka masu alaƙa da rashin abinci mai gina jiki kamar ƙarancin jini sun yawaita, in ji Abdu.
“Wannan raunin da aka haddasa ya bar al'umma ba tare da wata damar da za su iya jure duk wani katsewar taimako ba,” in ji shi. “Lokacin da Isra'ila ta rufe iyakokin shiga da fita, babu wani madadin gida ko damar samar da kayan buƙata da za su rage tasirin matsalar. A lokaci guda, Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai da rushe gonaki, tana lalata tushen abinci na Gaza.”
Matsalar ta ƙara tsananta a ranar 9 ga Oktoba, 2023, lokacin da Isra'ila ta ayyana “kulle gaba daya” a Gaza, ta katse abinci, ruwa, mai, da wutar lantarki. Shigo da kaya ya tsaya cak dare ɗaya, motocin taimako sun tsaya a kan iyaka, kuma ƙarancin kayan buƙata ya ƙara tsananta nan take.
Yayin da aka hana mai, wuraren yin burodi sun rufe, famfunan ruwa sun daina aiki, kuma motocin ɗaukar kaya sun tsaya. An gaza yi, ajiya ko isar da burodi. Ruwa mai tsafta ya ɓace, wanda ya ƙara jefa mutane cikin yunwa da cututtuka.
Abdu ya kuma nuna yadda aka lalata gonaki da haramta kamun kifi, yana kiran hakan wani ɓangare na tsarin Isra'ila na kawar da tushen abinci a Gaza.
“Mamayar ta juya raunin da ta ƙirƙira tsawon shekaru zuwa makamin kisan mummuƙe,” in ji shi.
Tilasta ƙaura na dagula matsalar yunwa
Umarnin Isra\ila na ƙauracewa yankunan Gaza, tare da ruwan bambamai sun tilasta wa dubban mutane tserewa, ta cunkoso a matsugunai shi ma ya taƙaita wadatar kayan abinci.
A halin yanzu, kiyasin Falasɗinawa miliyan 2 suna cikin halin rasa matsuguni a yankin da aka mamaye.
Abdu ya ce, “Tashi ba shiri yana haifar da mutane su rasa komai”.
Yara da mata masu ciki sun cikin waɗanda abin ya fi shafa. Yunwar ta ƙara tsananta saboda cutuka da ƙarancin ruwa bai tsafta, wanda ya haifar abin da Abdu ya kira “cikakkiyar matsalar abinci, lafiya, da haƙƙin samun gida.”
Zuwa farkon 2024, Isra’ila yana tsananta kamfe kan cibiyar jin-ƙai ta Gaza, Hukumar MDD kan Jin-ƙai da Ayyuka ga ‘Yan Gudun-Hijirar Falasɗinu a Near East.
Dakatar da ba da taimako ya gurgunta hukumar, an kai wa ɗakuna ajiyarta bam, an tare motocinta, sannan an samu rahotannin wawashe ɗakunan.
Isra’ila ta toshe kayan jin-ƙai zuwa arewacin Gaza daga farkon 2024, sun kuma tsaurara takunkumi bayan harin Oktoba, sannan ta rufe Rafah— mashigar ƙarshe ta Gaza — a Mayu.
Shekara ɗaya bayan nan, a Mayun 2025, Isra’ila tare da taimakon Amurka, ta ƙaddamar da shiri mai cike da ruɗani, wato Gaza Humanitarian Foundation (GHF) to saka ido kan aikin ba da taimako.
Maimakon maido da iso, MDD da manyan ƙungiyoyin sa-kai sun tir da da saka soji a harkar jin-ƙai, kuma sun bayyana kafa “yankunan jin-ƙai” a matsayin “tarkon mutuwa.” Tun lokacin, sama da Falasɗinawa 1,760 aka kashe yayin da suke yunƙurin karɓar abinci, kusan 1,000 cikinsu kusa da cibiyoyin GHF, cewar ofishin haƙƙin ɗan-adam na MDD.
“Bibiyar ayyuka Isra’ila da kalamanta — tsawaitar hana shiga, da rufe mashiga, ta tare motoci, da harar ɗakuna ajiyar abinci, lalata gonaki, haramta yin su, da lahanta aikin UNRWA, da wawashe kayan jin-ƙai, hare-hare kan farar hula masu karɓar abinci, hari kan ‘yan-sanda da jami’an kariya, maimaita haramtaccen umarnin tserewa da kuma ma ƙirƙirar shirin Gaza Humanitarian Foundation — ya nuna salo ƙuru-ƙuru,” cewar Abdu.
“Wannan ba ruɗani ne da ya faru siddan ba amma assasa shi aka yi da gangan na yunwatarwa.”
Yunwatarwa, amma ba mataki mai tasiri
Ran 22 ga Agusta, shirin Food Security Phase Classification (IPC) ya faɗa a hukumance cewa akwai yunwa a sassan Gaza, wanda ke nufin an cimma manyan matakai uku — matsanancin hana abinci, mace-mace saboda matsanancin rashin gina jiki.
Cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, mace-macen Falasɗinawa mai alaƙa da yunwa da yunwatarwa sun kai aƙalla 460, ciki har da yara sama da 150.
Matsanancin yanayin ya bar duk mutum guda cikin biyar cikin halin rashin gina jiki a birnin Gaza, inda abin ke ƙaruwa kullum.
“Ko da bayan an ayyana yunwa, babu matakan gaske da aka ɗauka. Al’ummar duniya ta gaza tilasta wa Isra’ila, wadda ke ci gaba da taka ƙudurorin Majalisar Ɗinkin Duniya tare da goyon bayan Amurka da Turai,” in ji Abdu.
Ya ƙara da cewa ayyana yunwa yana da alfanu musamman wajen ƙarfafa daidaiton shari’a da bin daidai, sannan yana kafa kadarkon nuna adalci kafin cibiyoyi kamar Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ko Kotun Duniya (ICJ).
“A dokar jin-ƙai ta duniya, irin wannan yunwatarwa da gangan daidai take da laifin yaƙi. Yayin da ake da ƙaruwar hujjoji na niyya da sakamakon niyya, waɗannan ayyuka sun cika sharuɗɗan kisan ƙare-dangi,” cewar Abdu.
‘Ba abin da aka yi’
A Satumba, wani kwamitin MDD kan Yankin Falasɗinu da aka Mamaye, ciki har da Gabashin Jerusalem, a Isra’ila ya yanke cewa Isra’ila ta aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.
Bayan shekaru biyu na bincike, kwamitin ya ce hukumomin Isra’ila da jami’an tsaro sun aikata ayyuka huɗu ko biyar na kisan ƙare-dangi yadda aka ba da ma’anarsa a Yarjejeniyar Kisan Ƙare-Dangi ta 1948 Genocide Convention — kisan kiyashi, wanda ya haddasa lahanin jiki ko na tunana, haddasa yanayin rayuwa da gangan don kassara Falasɗinawa, da hana su haihuwa.
Kwamitin ya yanke cewa “Ƙasar Isra’ila tana da alhaki kan gaza hana kisan ƙare-dangi, kuma aikata kisan ƙare-dangi don hukunta masu aika kisan ƙare-dangi kan Falasɗinawa a Gaza.”
Sanarwar 16 ga Satumba ta ce, “Ya wajaba Isra’ila ta kawo ƙarshen tsarin yunwatarwa, ta ɗage ƙawanyar da ta yi don kyautata tabbatar da cikakkiyar samuwar kayayyakin jin-ƙai da shigar jami’an MDD, ciki har da UNRWA da OHCHR, tare da amincewa da cibiyoyin jin-ƙai na ƙasa-da-ƙasa da shirya bayar da kayayyakin agaji”.
Abdu ya jaddada cewa wannan shela tana da alfanu amma tana buƙatar ƙarfin hali da ɗabbaƙawa.
“Ayyana ayyukan Isra’ila a matsayin kisan ƙare-dangi ya kamata ya janyo ɗaukar alhaki ƙarƙashin Yarjejeniyar 1948 Genocide Convention, ciki har da karewa da hukuntawa. Ya kamata wannan ya tabbatar da matsin lambar siyasa da shari’a don ganin an isar da agaji,” in ji Abdu.
“Sai dai kuma a aikace, abin da aka yi kaɗan ne.”