Majalisar Dattawan Nijeriya ta yanke shawarar kafa kwamitin hadin gwiwa na wucin gadi tsakanin Majalisar Dattijaida Majalisar Wakilai domin magance karuwar hare-haren kyamar baki da ake kai wa ’yan Nijeriya a Afirka ta Kudu.
Kwamitin, wanda Shugaban Majalisar Dokoki zai jagoranta, zai kai ziyara ta bincike da ta diflomasiyya zuwa Afirka ta Kudu domin nemo mafita mai ɗorewa ga wannan matsala.
A cikin ayyukan, ana sa ran tawagar kwamitin za ta ziyarci Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu domin bayyana rashin jin dadin Nijeriya kan hare-haren da ake zargin ana kai wa.
Majalisar Dattijan kuma na shirin rubuta wasika ga Kakakin Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu, tare da gayyatar Ministan Harkokin Waje domin ya yi wa ’yan majalisa bayani kan sakamakon tattaunawar.
Haka kuma, Majalisar ta amince da kudurin Sanata Simon Lalong na sake duba yarjejeniyoyin da aka cim ma a taron hadin gwiwa na 2019 tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu, domin tabbatar da an aiwatar da su.
A gefe guda, Sanata Adams Oshiomhole ya ba da shawarar soke lasisin aiki na kamfanonin Afirka ta Kudu kamar MTN da DSTV a Nijeriya, amma an yi watsi da wannan shawara bisa ka’idojin majalisa.
A jawabinsa, Shugaban Majalisar Dattawa ya jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware matsalar, yana mai cewa daukar matakin tattalin arziki kan kamfanoni ba shi ne mafita mafi dacewa ba.
Ya kuma bayyana cewa Majalisar na daukar hare-haren da muhimmanci kuma za ta dauki matakin gaggawa.
Wadannan matakai sun biyo bayan kudirin gaggawa mai muhimmanci na kasa da Sanata Bassey ya gabatar mai taken: “Karuwar tsanantawar kyamar baki kan ’yan Nijeriya a Afirka ta Kudu da Ghana: kira ga daukar matakin gaggawa na kasa, diflomasiyya da jinƙai domin kare mutunci, tsaro da darajar ’yan Nijeriya.”
Yayin tattaunawar, ’yan majalisa sun samu sabani kan ko a janye kudirin domin tattaunawa a sirrance, bayan da Sanata Aliero ya bukaci hakan. Sai dai Sanata Ningi da wasu sun dage cewa a tattauna batun a fili.
’Yan majalisa sun nuna matukar damuwa ba kawai kan hare-haren ba, har ma da yanayin tsoro, da damuw da wulakanci da ’yan Nijeriya ke fuskanta a kasashen waje. Sun kuma lura cewa ana ƙara ware ’yan Nijeriya da kai musu hari saboda asalinsu kawai.
Daga bisani, Majalisar Dattawa ta yi shiru na minti guda domin girmama ’yan Nijeriya da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren a Afirka ta Kudu.










