Tinubu ya yi ganawar sirri da manyan jami'an tsaron Nijeriya

Da yake bayani ga manema labarai bayan ganawar, babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya Waidi Shaibu ya ce sun samu labari mai kyau daga jihar ƙwara inda mutane 38 da aka yi garkuwa da su daga cocin suka koma ga iyalansu.

By
Shugaba Tinubu ya yi wannan ganawar ne a ranar Lahadi da dare

Shugaba Tinubu ya yi ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaro na Nijeriya a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

Ganawar da suka yi ranar Lahadi ta samu halartar babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyode da babban hafsan sojin saman Nijeriya, Air Vice Marshal Kelvin Aneke da babban hafsan sojin ruwan Nijeriya, Rear Admiral Idi Abbas da kuma babban hafsan tattara bayanan sirrin sojin Nijeriya, Manjo Janar EAP Undiendeye ba babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya, Manjo Janar Waidi Shaibu.

Kazlika waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, da babban darakatan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Tosin Ajayi.

Da yake bayani ga manema labarai bayan ganawar, babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya Waidi Shaibu ya ce sun samu labari mai kyau daga jihar ƙwara inda mutane 38 da aka yi garkuwa da su daga cocin suka koma ga iyalansu.

“Kuma an samu ci gaba a jihar Neja inda kimanin mutum 51 daga cikin ɗaliban suka koma ga ‘yan wansu. A jihar Kebbi, matakanmu na samun sakamako mai kyau. Ana samun ci gaba sosai a wannan fannin,” a cewar Janar Shaibu.

 “Kuma dukkannin jam’ian tsaro suna wurin inda suka zagaye dukkan wurin. Inda muke tsammanin za mu samu labari daga wannan wurin,” in ji shi.

Shi ma shugaban Nijeriyar, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ganawar ta yi nazari kan rahotanni na baya bayan nan da kuma ɗaukar ƙwararan matakai domin tabbatar da zaman lafiya a yankunan.

“Ina ci gaba da samun bayanai kuma na ba da umarni ga hukumomin tsaronmu su ɗauki mataki cikin sauri da seti da kuma jajircewa,” in ji shugaban ƙasar a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“A matsayina na shugaban ƙasa, na jajirce sosai a kan tsaron ‘yan Nijeriya. Waɗanda suke barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasarmu, za su fuskanci cikakkiyar uƙubar doka,” a cewar shugaban ƙasar.

Cikin ‘yan ƙwanakin nan dai Nijeriya ta fuskanci hare-haren ‘yan ta’adda da suka sace mutane a jihohin Kwara da Kebbi da Neja.

A jihar Kwara dai, ‘yan bindiga sun sace mutane a lokacin da suke ibada a wani coci da ke garin Eruku.

A jihar Kebbi kuma ‘yan bindiga sun saci ɗalibai 25  ‘yan makarantar sakandare ta ‘yan mata ta GGCS da ke garin Maga. Biyu daga cikin ɗaliban sun kuɓuce daga hannun masu garkuwa da mutane.

Sai kuma jihar Neja inda ‘yan bindiga suka saci mutum 315 a makaranatar firamare ta ɗarikar Katololika inda daga baya 50 daga cikinsu suka kuɓuce kuma suka koma ga iyalansu.

 Sai dai shugaban ƙasar ya yi shelar cewa an ‘yanta mutum 38 da aka yi garkuwa da su a jihar Kwara kuma ya sha alwashin cewa zai yi abin da ya dace domin tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya.