Ɗan wasan Madrid, Mastantuono ya kamu da cutar matsematsi irin wadda Yamal ke fama da ita

Matashin ɗanwasan Real Madrid, Franco Mastantuono ya bayyana yadda yake fama da cutar matsematsi ta Pubalgia, irin wadda take damun Lamine Yamal da ma wasu matasan 'yan wasa a Turai.

By
Franco Mastantuono na da shekaru 18 a duniya

Matashin ɗanwasan Real Madrid, Franco Mastantuono ya bayyana yadda yake fama da cutar matsematsi ta Pubalgia, irin wadda Lamine Yamal ke fama da ita.

Mastantuono wanda ya zo Madrid daga River Plate a bazarar bana ya fara samun gurbi a tawagar da Koci Xabi Alonso ke jagoranta, kafin jinya ta dakatar da shi.

Ɗanwasan ɗan asalin Argentina ya yi bayani kan cutar Pubalgia, wadda take kawo masa cikas tun makonnin baya-bayan nan, kamar yadda take damun Yamal.

Lokacin da ya zo Real Madrid kan dala miliyan 53, Mastantuono mai shekaru 18 ya shiga jerin matasan da ake ganin suna da damar samun tagomashi cikin sauri.

Tun a makon farko na kakar bana Alonso ya fara saka shi, kuma ya samu karɓuwa cikin tawagar har ya ci ƙwallo guda da tallafin ƙwallo ɗaya a wasanni 12 da ya buga.

Sai dai, matsalar matsematsi ta hana Mastantuono sakat, saboda tana haifar masa da raɗaɗi a ƙasan ciki da mara, wanda ke iya zuwa kowane lokaci.

Mece ce Pubalgia?

Cutar Pubalgia wadda kuma ake kira ƙarin masu wasanni, tana jerin cutuka masu tsauri ga ‘yan wasa da ke buƙatar zafin nama da hanzarin motsi.

Takan shafi mahaɗar tsakanin mara da tsokar jijiya, kuma jinyarta kan ɗauki makonni. ‘Yan wasan gefe da ke yawan yin juyi da zabura sau da dama sun fi shiga haɗari.

Cuta ce da ba a mata garaje wajen jinya saboda idan ɗan wasa ya koma fili da gaggawa, ciwon zai dawo sabo.

Ɗanwasan ya bayyana cewa zogin a hankali yake farawa, sai ya yi ta ci gaba har mutum ya kasa jurewa. Kuma tun yana tsohon kulob ɗinsa na River Plate ta fara damun sa.

Ya ce, "Ciwo ne da na kwana-biyu yana damu na. Lokaci ya yi da zan rage aiki har na samu sauƙi sosai don na iya aiki ɗari bisa ɗari. Kulob ɗin na buƙatar hakan. Zan dawo wasa nan kusa."

Baya ga Franco Mastantuono, Lamine Yamal na Barcelona, Nico Williams na Athletic, da Cole Palmer na Chelsea, waɗanda masu ƙarancin shekarun ne, duka suna fama da cutar.