Kafafen watsa labaran Afirka: Abokan kawo ci gaba da ake mantawa da su

Muna bukatar sabon hadin kai tsakanin kafafen watsa labarai da masu kawo cigaba. Hadin kai na gaskiya, amana da biyan bukatun bai daya masu fifiko. Hadin kan da kafar watsa labarai za ta zama bokiyar kawo ci gaba, ba mai aike wa da sakonni kawai ba.

By
'Yan jaridar Afirka sun taru a hedikwatar Tarayyar Afirka a Addis Ababa don halartar Taro. /Photo: UNDP Africa/Ugochukwu Kingsley Ahuchaogu

Afirka ba ta fama da ƙarancin tunani mai kyau. Kuma ba ta karancin buri ko ƙudurin kawo cigaba.

Amma labarin Afirka sau da yawa ana bayar da a gutsittsire: kanun labarai game da rikici a nan, ƙididdiga game da talauci a nahiyar, bikin kirkire-kirkire ko matasa a wani waje.

Samar da cigaba fiye da wannan yayyanka labarin na buƙatar gaskiya da tunani mai zurfi.

Tafiyar ci gaban Afirka ta kasance mai cike da ƙalubale - kuma yayin da ci gaba ke buƙatar aiki a fannoni da yawa, dawo da bayar da labarinmu da kanmu ya zama dole cikin gaggawa.

Wannan zai iya faruwa ne kawai ta hanyar tsarin kafofin watsa labarai wadanda ke nuna cikakkiyar gaskiya game da Afirka: gwagwarmayarta, juriyarta, nasarorinta da damarmakin da take da su.

Afirka za ta iya - kuma ya kamata - ta yi mafi kyau. Haka ne, akwai abubuwa da yawa da za a yi murnarsu: kaifin basira, juriyarmu da ƙarfinmu na matasa. Amma dole ne mu kuma kasance masu gaskiya game da inda muka tsaya.

Makonni kaɗan da suka gabata, UNDP ta fitar da Ma'aunin Talauci Mai Fadi. Sakamakon binciken ya yi tsauri: sama da mutane biliyan ɗaya a duniya suna rayuwa cikin talauci.

Abin mamaki shi ne inda talaucin yake - kusan miliyan 740 ko kashi 64.5 na talakawa masu fama da talauci mai tsauri na zaune a ƙasashe masu matsakaicin samun kuɗade.

A takarda, waɗannan ƙasashe suna kan turba mai kyau. Amma a bayan alkaluman GDP akwai gidaje da ke gwagwarmaya, matasa sun rasa damarmaki tare da tsarin da ke cikin mawuyacin hali.

Alƙaluman ba su ƙare a nan ba. Yanzu Afirka tana kashe kusan dala biliyan 90 a kowace shekara don biyan basussukan kasashen waje.

Ƙasashe masu tasowa, ciki har da da yawa a Afirka, suna buƙatar kimanin dala tiriliyan 4.2 don cike gibin kuɗi don Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa.

Waɗannan alkaluma sun nuna mana cewa shingen da ke tsakanin buri da ikon aiwatarwa na da faɗi - kuma ana jin sakamakonsa a kowace al'umma da kowane tsarin tattalin arziki.

Wannan shi ne ainihin gabar da kafofin watsa labarai ke shigo wa.

Kalubalenmu suna buƙatar ingantaccen rahoto kuma wanda ke da jagoranci daga gida - amma haka ma mafitarmu.

Labarun da muke bayarwa, shaidar da muke gabatarwa, da hotunan da muke nunawa suna tsara fahimtar jama'a da yanke shawara kan manufofi.

Lokacin da muka nuna abin da ke aiki, masu tsara manufofi suna sauraro. Lokacin da muka rubuta abin da ya yi rashin nasara, 'yan ƙasa suna zabura.

Ganin kafofin watsa labarai a matsayin masu lura da abubuwan da ba sa so a cikin labarin ci gaban Afirka abu ne tsoho - kuma kuskure ne. Fahimtar kafofin watsa labarai a matsayin wakilan canji a kashin kansu

Ka yi la'akari da isa ga yanayin kafofin watsa labarai na yau. Shiga intanet har yanzu yana iya zama ƙasa da kashi 40 cikin ɗari a faɗin nahiyar, amma yana ƙaruwa da sauri. Kusan rabin dukkan 'yan Afirka suna da wayar hannu. Samun damar shiga talabijin har yanzu na da yawa.

Bari mu ɗan yi tunani game da yadda waɗannan kayan aikin suke da ƙarfi - ba wai kawai don raba bayanai ba, har ma don yin tasiri ga manufofi da zaɓuɓɓuka waɗanda ke ƙayyade yadda muke rayuwa, aiki da habaka.

Dole ne mu yi amfani da su da kyau - kuma dole ne mu yi hakan da gaggawa wanda ya dace da gudun lokaci a zamaninmu.

Ta yaya za mu yi hakan? Muna bukatar sabon hadin kai tsakanin kafafen watsa labarai da masu kawo cigaba.

Hadin kai na gaskiya, amana da biyan bukatun bai daya masu fifiko. Hadin kan da kafar watsa labarai za ta zama bokiyar kawo ci gaba, ba mai aike wa da sakonni kawai ba.

Aboki mai nuna kuskure. Murya mai zaman kanta. Mai sanya idanu da bin diddigi. Mai tsara mafita.

Mai wadataccen karfi da aka samar, Wadanda ake girmama wa da yi wa kallon ginshikin samar da cigaban Afirka, ba wai kafafen isar da sakonni kawai ba.

A UNDP, muna fifita saka hannun jari a cikin wannan haɗin gwiwar. Wannan yana nufin aiki tare da kafofin watsa labarai da wuri, sauraron abin da suke gani, da kuma mayar da martani lokacin da suka nemi karin bayani. Yana nufin daraja fahimtar da ba wai kawai wadda ta fito daga bayanai ba, har ma da gogewa ta rayuwa.

Daga tattaunawar da na yi kwanan nan da 'yan jaridar Afirka da masu ba da labarai a wajen Taron ‘UNDP Africa Media’ a Addis Ababa, a bayyane yake cewa ba kaifin kakwalwa ba ne matsalar. Akwai aniya mai kyau.

Abin da ake buƙata shi ne fahimtar juna cewa idan muna son hanzarta ci gaban Afirka, dole ne mu kuma hanzarta yadda muke ba da labarinta.

A ƙarshe, ana tsara zaɓin manufofi - kuma suna da tasiri - ta hanyar fahimta. Kuma idan muna son wata makoma daban ga nahiyar, dole ne mu fara sake tunaninta - kuma mu faɗi hakan ga duniya - ta hanya ta daban.

Marubucin, Dr. Jide Okeke, shi ne Daraktan Shirin UNDP a Shiyyar Afirka.

Togaciya: Ba lallai ra’ayoyin da marubucin ya bayyana ya zama sun dace da ka’idojin dab’i na TRT Afrika ba.