‘Yan bindiga sun sace ɗalibai da ma’aikata a wata makaranta a Jihar Neja
Bayanai na cewa, maharan sun afka makarantar ne da misalin karfe biyu zuwa uku na dare, inda suka tafi da dalibai da ma’aikatan, sai dai har kawo yanzu babu bayani kan adadin mutanen da harin ya shafa.
Rahotanni daga Jihar Neja a arewa ta tsakiyar Nijeriya na cewa, yan bindiga sun sace daliba da ma’aikatan wata a Makarantar St. Mary a karamar hukumar Agwara a Jihar Neja cikin daren Juma’a.
Kawo yanzu babu cikakken bayani kan adaddin mutanen da aka sace, sai dai gwamnatin jihar ta Neja ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ta fitar, sai dai ba ta yi karin bayani ba.
Ita ma rundunar ‘yan sandan jihar ta Neja ba ta kai ga fitar da bayani kan lamari ba, sai dai kakakin runduna ya shaida wa manema labarai a kasar cewa zai bayar da cikakken bayani nan gaba.
Bayanai na cewa, maharan sun afka makarantar ne da misalin karfe biyu zuwa uku na dare, inda suka tafi da dalibai da ma’aikatan.
Sace daliban a makaranta a jihar neja dai na zuwa ne kasa da mako guda da sace wasu dalibai mata 25 a makarantar sakandaren gwamnati a Jihar Kebbi, da kai hare-hare a jihar Kwara, abin da ya tilasta rufe makarantu fiye da 50 a Jihar ta Kwara.