Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya, EFCC, ta sanar da bayar da ladan kuɗi tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 ga duk wanda ya samar mata da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano tare da ƙwato kuɗaɗe da kadarorin Nijeriya da ake zargin an ɓoye a ƙasashen waje.
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-sheraka karo na 43 kan Laifukan Tattalin Arziki da ake gudanarwa a Cambridge na kasar Birtaniya, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya fitar a ranar Laraba ta yi nuni.
A cewar sanarwar, Olukoyede ya buƙaci duk wanda ke da sahihan bayanai game da kadarorin Nijeriya da ake zargin an fitar da su zuwa ƙasashen waje ta haramtacciyar hanya ya tuntubi hukumar.
Ya ce, waɗanda suka samar da bayanan da suka kai ga nasarar ƙwato kadarorin za su samu ladar da ta kai tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na kimar kadarorin da aka ƙwato.
Olukoyede ya ce tukwicin na iya mayar da waɗanda suka samar da sahihin bayanai miloniya, gwargwadon darajar kadarorin da aka gano kuma aka ƙwato sakamakon bayanin da suka bayar.
Ya bayyana cewa an samar da tsarin ne domin inganta damar EFCC ta samun bayanai masu tushe da ƙuma ƙarfafa ƙoƙarin gano da kuma ƙwato kadarorin ƙasar da aka fitar daga Nijeriya ta ba bisa ƙa’ida ba.
Shugabn na EFCC ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙwato kadarorin da kimarsu ta kai dala miliyan 500 wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya cikin shekara uku na shugabancinsa na hukumar.
Ya alaƙanta ƙwato kadarorin da ƙwarewar masu binciken EFCC ɗin da ɓangaren shari’a da ke taimakawa da kuma damar samun bayanan sirri masu tushe.





















