Gwamnantin Mali ta yi ƙarin haske game da kisan Ministan Tsaron ƙasar Sadio Camara, tana mai cewa ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu yayin da yake musayar wuta da 'yanta'adda waɗanda suka kai hari gidansa.
A wata sanarwa ta gwamnati da Ministan Ƙasa kuma kakakin gwamnati Issa Ousmane Coulibaly ya karanta a gidan talbijin na ƙasar, ya ce wani ɗan-ƙunar-baƙin-wake a cikin mota ne ya tashi bama-baman da ke jikinsa a cikin gidan minista da ke garin Kati, wani muhimman gari mai cike da sojoji da ke kusa da Bamako, babban birnin ƙasar.
Rahotanni sun ce Camara ya fafata da ‘yanta’addan inda ya “kawar da dama daga cikinsu” kafin su jikkata shi.
Daga bisani aka garzaya da shi asibiti amma rai ya yi halinsa.
Gwamnati ta ƙara da cewa rushewar da gidan ministan ya yi ta yi sanadin mutuwar ƙarin mutane da kuma ruftawar wani masallaci da ke kusa, inda a can ma mutane da ke sallah a lokacin suka mutu.
“A wannan mawuyacin hali, Janar Assimi Goita, shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya kuma Kwamandan Askarawan Malian, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin,” in ji sanarwar.
Kazalika shugaban ƙasar ya miƙa saƙon ta’aziyya ga dukkan fararenhula da sojoji da suka mutu a hare-haren da aka kai ranar 25 ga Afrilu.













