Messi ya ce cutar rashin girma ce ta hana kungiyoyin Argentina daukarsa sanda yana yaro

Gwarzon ɗan ƙwallon Argentina, Lionel Messi ya bayyana kulob ɗin da ya so buga wa sanda yana yaro, amma sai ƙungiyoyin Argentina suka ƙyamace shi saboda tsadar kuɗin maganin cutar hana girma da ke damunsa.

By
A yanzu Messi yana da shekaru 38, amma yana fatan komawa ƙwallo Barcelona / AP

Saɓanin yadda masoya Barcelona suka yi tunanin, gwarzon tsohon ɗanwasan ƙungiyar, Lionel Messi ya ce ba Barca ce inda ya yi burin buga wa wasa ba sanda yana yaro.

Messi ya bayyana cewa gabanin shigarsa Barca, manyan ƙungiyoyi ƙwallo a Argentina da dama, irinsu River Plate sun guji ɗaukar sa saboda tsadar kuɗin maganin cutarsa ta hana girma.

Ranar 14 ga Disamban 2000 ne daraktan wasanni na Barcelona, Carles Rexach, ya sha alwashin ɗaukar Messi sanda yana shekara 13.

Bayan ya je wasan gwaji a Barca, ba tare da ya samun saƙo kan matsayarsa ba, dangin Messi sun yi tunanin gwada sa’a a Real Madrid da Atletico Madrid.

Messi ya bai fara buga wasa a Barcelona ba sai a 16 ga Nuwamban 2003, a wani wasan sada-zumunta tare da Porto. Sanda ya kai shekara 17 ya buga wasan LaLiga ran 16 ga Oktoba.

Kulob ɗin yarinta

Lionel Messi ya bayyana a wata hira da ESPN cewa, "Na kasance ian burin cewa burina na buga wasa a babban kkulob ɗin Newell. Nakan je filin wasansu na buga ƙwallo ina mai burin zama ƙwararren ɗanwasa a gasar Primera.

Ya ƙara da cewa, “Kwatsam sai rayuwata ta canja gabaɗaya ina shekara 13, na shiga Barcelona, kuma dukmabin da ya faru bayan nan.“

A Barcelona dai, Messi ya kafa tarihi kala-kala ciki har da cin ƙwallaye 672 a wasanni 778, tare da lashe kofunan La Liga har guda 10 da na Zakarun Turai guda 4.