Nijeriya da Tunisia za su ɓarje gumi a wasansu na biyu na Gasar AFCON 2025
Kowanne cikin Nijeriya da Tunisia ya ci wasansa na farko, don haka a maraicen Asabar kowa zai yi ƙoƙarin samun nasara a wasa na biyu don wucewa zagaye na gaba a Rukunin C.
A ci gaba da Gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta AFCON 2025 da ke gudana a Maroko, da maraicen Asabar Nijeriya za ta kara da Tunisia a wasa na biyu na Rukunin C.
A wasan farko a rukunin, Nijeriya ta doke Tanzani da ci 2-1, yayin da Tunisia ta doke Uganda da ci 3-1, inda kowa ya samu maki uku kenan.
Don haka kowace ƙasa za ta yi ƙoƙarin samun nasara don haye wa saman teburi tare da wucewa zagaye na gaba.
Za a buga wasan ne da ƙarfe 9 na yamma agogon birnin Fas (ƙarfe 7 na yamma agogon Nijeriya), a filin wasa na Complexe Sportif de Fes na birnin da ke arewacin Maroko.
A tarihi, ƙasashen biyu sun fara haɗuwa ne a 1961, inda suka buga wasa karo biyu don neman cancantar buga gasar Kofin Afirka ta 1962.
Nijeriya ta ci wasan gida da ci 2–1, amma a wasan ramako a Tunisia sai da ana wasa ci 2–2, sai Nijeriya ta fice daga wasan, inda aka bai wa Tunisia nasara da maki 2–0, da jimillar ci 3–2.
Daɗewa ba a haɗu ba
Haka nan Nijeriya da Tunisia sun haɗu a wasannin neman cancantar buga gasar kofin duniya na FIFA har sau huɗu: 1978, 1982, 1986, da 2010.
A 1978, Tunisia ta yi nasara kan Nijeriya, sannan a 1982 Nijeriya ta yi nasara, sai a 1986 Tunisia ta yi nasara, sannan kuma a 2010 Nijeriya ta yi nasara.
A gasar AFCON kuwa, Nijeriya da Tunisia sun haɗu karo shida inda Nijeriya ta yi nasara sau uku, Tunisia ta yi nasara sau ɗaya.
Sun yi canjaras sau biyu, a wasanni da sai da ake je bugun fanareti sannan kowa ya ci karo ɗaya.
Karo na ƙarshe da ƙasashen suka kara da juna shi ne a zagayen ‘yan-16 na AFCON 2021, inda Tunisia ta doke Nijeriya da ci 1–0.