Isra’ila ce ummul aba'isin haramtaccen yaƙi da Iran: In ji Erdogan na Turkiyya
Shugaba Erdogan ya yi gargadi kan karuwar rikicin yanki, yana mai cewa Turkiyya na da manufar fita daga kangin ba tare da cutuwa ba kuma da nesanta daga kurar yakin.
Gwamnatin Isra’ila ce mai babban alhakin ‘haramtaccen yakin’ da ake ci gaba da yi kan Iran, in Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyiip Erdogan.
"Gwamnatin Isra'ila ce ke da alhakin wannan yaƙin da ba ya bisa ƙa'ida, wanda ba wai kawai ya mayar da yankinmu yankin rikici ba, har ma janyo wa dukkan bil'adama wahala a fannin tattalin arziki," in ji Erdogan a ranar Laraba, yayin da yake jawabi a taron 'yan majalisar jam'iyyarsa ta Adalci da Ci Gaba (AK) a babban birnin Ankara.
"Bai kamata a manta da cewa kowane digo na jini da aka zubar a yakin zai tsawaita rayuwar siyasa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba," in ji shi.
Erdogan ya ce rikicin da ya fara a ranar 28 ga Fabrairu a yankin ya cika watansa na farko kuma yana ci gaba da ƙaruwa da barazanar da hatsari, ya ƙara da cewa fifikon Turkiyya shi ne ta wuce wannan lokaci mai cike da rikici ba tare da wata illa ba kuma ta ƙuduri aniyar nisantar da ƙasar daga wutar rikicin.
"Daga cikin manyan hatsarin da yankinmu ke fuskanta ba wai kawai tsawaita yaƙin ba ne, har ma da hatsarin rikidewa zuwa faɗaɗar rikicin yanki, yayin da hare-haren ramuwar gayya da ke kai hari kan cibiyoyin makamashi, sufuri, da kayayyakin more rayuwa na fararen hula ke ƙara yawan yiwuwar hakan," in ji shi.
Ya ce Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya halarci wani taro na bangarori hudu a Islamabad tare da takwarorinsa na Saudiyya, Masar, da Pakistan, inda aka tattauna matsalolin da ake fuskanta, sannan aka duba matakan da za a dauka don kawo karshen yakin.
Ya kara da cewa Ministan Tsaron Kasar Turkiyya Yasar Guler da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (MIT) Ibrahim Kalin, da sauran jami'ai su ma suna yin kokari sosai a fannoni daban-daban.
"Idan akwai ɗan ƙaramin fata na kawo ƙarshen zubar da jini, don kawo karshen yakin da daina zubar da hawaye, da kuma warware matsaloli ta hanyar diflomasiyya, wajibi ne mu kwaci damar aiki fatan," in ji shi.
"Tun farkon yaƙin, matsayin Turkiyya, halinta, da saƙonnin da ta aika wa duniya da yankin sun kasance muryar ɗan adam da tunani mai kyau," in ji shi.
Yaƙi da Iran ba shi zai cika burin zaman lafiya a duniya ba, sai dai ya ma lalata shi, in ji Erdogan, yana mai jaddada cewa diflomasiyya, tattaunawa, da sulhu su ne manyan kayan aiki da ake da su don gujewa wannan rashin jituwa, yana mai jaddada buƙatar neman daidaito maimakon dagewa kan buƙatu masu ƙarfi.
"Fatanmu shi ne a buɗe hanyar zaman lafiya ba tare da ƙarin zubar da jini ba, kuma don haka, za mu ci gaba da yin duk abin da za mu iya, ko da kuwa hakan na nufin sanya kanmu a kan layi," in ji shugaban Turkiyya.