Real Madrid ta sallami Xabi Alonso, ta nada Alvaro Arbeloa sabon koci

Real Madrid ta sallami kocinta Xabi Alonso watanni bakwai bayan kama aiki, bayan Barcelona ta doke su a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup.

By
Xabi Alonso ya yi watanni bakwai ne yana jagorantar Real Madrid / Reuters

Kasa da awanni 24 bayan Barcelona ta doke Real Madrid a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup, ƙungiyar ta raba gari da kocinta Xabi Alonso.

Kocin ɗan asalin Sifaniya ya sha matsi a ‘yan makonnin nan sakamakon rashin tagomashi mai ɗorewa a wasannin da yake jagoranta.

Da ma an yi ta raɗe-raɗin cewa hukumomi a Madrid sun yanke shawarar korar Alonso matuƙar bai ciyo musu kofin ba a wasan da aka buga a ƙasar Saudiya a maraicen Lahadin da ta gabata.

Wata sanarwa daga Real Madrid ta ce Alonso ya bar kulob ɗin bayan sun samu daidaito tsakaninsu.

Hakan na zuwa ne bayan jan ragamar wasanni a ƙungiyar tsawon watanni bakwai kacal.

Madrid ta naɗa Alvaro Arbeloa mai shekaru 42, wanda abokin wasan Alonso ne sanda yana Liverpool. Arbeloa ya yi aiki a makarantar jorar da wasa ta Madrid tun 2020.

Haka nan ya kasance kocen ƙaramar tawagar B ta Real Madrid tun kakar bara.

Real Madrid ta gode wa Xabi Alonso tana mai cewa ƙungiyar za ta ci gaba da zama gida ga tsohon kocin.