Courtois ya jajanta wa golan Tottenham da aka ci ƙwallo 3 a minti 16 da fara wasa

Mai tsaron ragar Real Madrid, Thibaut Courtois, ya jajantawa golan Tottenham, Antonin Kinsky, wanda aka canja minti 16 da fara wasansa na farko a gasar Zakarun Turai ranar Talata.

By
Sau 13 kacal Antonin Kinsky ya buga wa Tottenham wasa tun bayan zuwansa a Janairun 2025. / Reuters

Golan Real Madrid, Thibaut Courtois ya sanar da cewa ya tuntuɓi golan Tottenham, Antonin Kinsky don jajanta masa kan abin takaicin da ya same shi a wasan Tottenham da Atletico Madrid ranar Talatar nan.

A wasan na gasar Zakarun Turai, an zura wa Kinsky ƙwallo 3 cikin minti 16 da fara wasa, inda koci Igor Tudor ya yanke hukuncin sauya shi a wasan da Atletico ta doke Tottenham da ci 5-2.

Courtois ya ce "Na gaya masa cewa ya koyi darasi daga wannan. Rayuwa tana da wuya amma dole ya zama mai ƙarfin hali. Matsayin gola yana da matuƙar sammatsi. Idan muka yi kuskure, yakan haifar da zura ƙwallo. Ina roƙon Tottenham ta tallafa masa."

“Ni ma na taɓa tafka kuskure a Atlético Madrid, na yi kurakurai a Chelsea, sau biyu Messi yana zura min osi," in ji Courtois wanda gwarzon gola ne a gasannin Turai.

A yayin wasa na zagayen ‘yan-16 a gasar Zakarun Turai, Kinsky ya samu damarsa ta farko ta buga wasa a gasar mai daraja, inda aka yi tunanin zai nuna bajinta don samun gurbi a tawagar.

Rashin tagomashi

Sai dai ana minti na 5 da fara wasan, Antonin Kinsky ya zame garin ƙoƙarin buga ƙwallo, inda aka ƙwace ƙwallon sannan a ƙarshe ɗanwasan Atletico, Marcos Llorente ya zura ta a ragar Tottenham a minti na 6.

Haka nan a minti na 15, ɗanwasan Atletico, Antoine Griezman ya zura wa Kinsky ƙwallo ta 2, Sannan a minti na 16, golan ya sake tafka kure yayin buga ƙwallo, inda Julian Alvaraz ya karɓe ƙwallon ya zura ta 3.

Ganin yadda aka ci su 3-0 tun ba a je ko ina ba, kocin Tottenham ya cire Kinsky, inda ya maye gurbinsa da Guglielmo Vicario.

Ko bayan tashi wasan, ana ambato Antoine Griezmann yana tausaya wa Kinsky kan cewa rashin sabo da santsin filin wasan ya janyo wa golan mai shekaru 22 zamewa yayin buga ƙwallo.

Da ma dai tun bayan zuwansa Tottenham daga Slavia Prague kan fam miliyan £12, sau 13 kacal Antonin Kinsky wanda ɗan asalin Czech ne, ya buga wa Tottenham wasa.

Tottenham dai na fama da babban ƙalubalen rashin tagomashi a kakar bana, inda a gasar Firimiya, take mataki na 16 da maki 29, wato maki ɗaya kawai ya raba ta da rukunin ƙungiyoyin da za a kora, yayin da wasa 9 ya rage a kakar.