| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
An fara shirin gasar Cin Kofin Duniya, yayin da ita ma tawagar Turkiyya ta isa Amurka
Haɗakar ƙwararrun shugabanni da taurari da ke haskawa, tawagar Crescent-Stars ta fara shirinta na ƙarshe gabannin shiga gasar Kofin Duniyar na farko cikin shekaru 24 .
An fara shirin gasar Cin Kofin Duniya, yayin da ita ma tawagar Turkiyya ta isa Amurka
Arda Guler na Turkiyya ya isa Amurka yayin da aka fara shirin fara gasar cin kofin duniya ta 2026 a Miami, Florida, Amurka, 2 ga watan Yuni, 2026. / Others

Tawagar ƙwallon ƙafar Turkiyya ta isa Amurka ranar Talata yayin da ta shiga mataki na ƙarshe na shirya wa gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2026.

Tawagar ta sauƙa a Fort Lauderdale, Florida, inda Babban Jakadan Turkiyya a Amurka Sedat Onal da ƙaramin Jakadan Turkiyya a ƙasar, Resul Sahinol, suka tarbi tawagar. 

Tawagar za ta buga wasan sada zumunta na ƙarshe da Venezuela kafin ta mayar da hankalinta Kacokan kan gasar.

Tawagar ta Turkiyya wadda Vincenzo Montella ne koicinta, za ta koma gasar cin kofin duniya a karon farko ne tun shekarar 2002, kuma ta shiga gasar da wasu ‘yanwasa da suka haɗa da keftin Hakan Calhanoglu da Arda Guler da kuma Kenan Yildiz.

Hankali ya koma kan rukunin D

Bayan wasan sada zumunta da Venezuela, Turkiyya za ta kafa sansanin gasar cin kofinta a Mesa, Arizona, kafin wasanta na rukunin D na farko da Australia.

Tawagar ta Crescent-Stars za ta kuma kara da Paraguay da Amurka da ke cikin ƙasashe masu masauƙin baƙi yayin da suke ƙoƙarin ficewa daga wani rukuni mai wahala .

Gasar Cin Kofin Duniyar da ƙasashen Amurka da Kanada da Mexico ke karɓar baƙunci, ta faɗaɗa zuwa ta tawagogi 48, kuma za a fara ta ne ranar 11 ga watan Yuni har zuwa ranar 19 ga watan Yuli.

Rumbun Labarai
Turkiyya da Nijeriya sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa kan ƙera jiragen ruwa
Shugaba Erdogan ya taya tawagar Sultans of Net ta Turkiyya murnar lashe gasar ƙwallon raga ta mata
Shugaba Erdogan ya yi taron cika shekaru shida da sake bude Hagia Sophia don Ibadar Musulmai
Ayyukan ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila na barazana ga ƙoƙarin zaman lafiya a Ƙudus: Turkiyya
Turkiyya ta yi kira ga Amurka da Iran su koma kan yarjejeniya, su kuma yi aiki tare da Qatar
Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5 ta auka wa gabashin Turkiyya
Ga yadda Turkiyya ke son hana ‘yan ƙasa da shekaru 18 shan taba sigari
Dangantakar Turkiyya da Afirka da yaƙi da FETÖ bayan yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli da aka daƙile
Matar shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta tuna da ranar murƙushe yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli
Daƙile yunƙurin juyin mulki na 2016 ya 'bayyana 'yancin kai' na ƙarni ga Turkiyya, in ji  Erdogan
Turkiyya na juyayin cika shekaru 10 da yunƙurin juyin mulki na ranar 15 ga Yuli da bai yi nasara ba
Turkiyya ta umarci makarantu su goge hotunan ɗaliban da aka wallafa ba tare da izinin iyaye ba
Jami’an leƙen asiri na Turkiyya sun kama wani babban jami’in Daesh a Syria
Manufofi da gwamnatin Netanyahu 'nauyi' ne ga Isra'ila da yankin da tsaron duniya: Ministan Turkiyya
Emine Erdogan ta karbi bakuncin matan shugabannin NATO don tattaunawa kan yara, fasaha da tsaro
Shugaba Erdogan ya ce taron NATO a Ankara ‘nasara ce ta tarihi’
Taron Trump-Erdogan: Amurka za ta ɗage wa Turkiyya takunkumai, za a yanke hukunci kan F-35 nan kusa
Tsaron Turai ba zai ta’allaka ga Tarayyar Turai ba, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan
Taron Koli na NATO a Ankara na nuna muhimmiyar rawar Turkiyya a harkar tsaro da diflomasiyyar duniya
Muhimmin labarin fursunonin yaki Turkawa da ya sauya fasalin aƙidun horon sojojin NATO