Jami’an tsaron Nijeriya sun kwance wani bam da ‘yan ta’adda suka dasa a Zamfara

Rundunar 'yansandan Nijeriya reshen jihar Zamfara ta ce jami’an tsaron sun yi amfani da hanyoyin ƙwarewa domin kwance bam ɗin wanda aka dasa a kan hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

By
Kungiyoyin ‘yanbindiga suna da sansanoni a cikin wani babban daji da ya ratsa jihohi da dama, ciki har da Zamfara / Others

Jami’an tsaro Nijeriya sun samu nasarar kwance wani bam da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa a kan hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

An gudanar da wannan aiki ne da haɗin gwiwar rundunar kwance bama-bamai da ababen fashewa ta ‘yansandan Nijeriya da Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane, da kuma rundunar EOD ta Sojoji, tare da cikakken tsaro daga Rundunar ‘Yansandan Nijeriya Reshen Jihar Zamfara.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Yazid Abubakar, ya fitar a ranar Asabar, ya ce aikin wanda aka gudanar ranar Juma’a, SP Abdulrazak Musa Hassan ne ya jagoranta shi.

Ya ce jami’an tsaron sun yi amfani da hanyoyin ƙwarewa domin kwance bam ɗin.

“An kwance sassan bam ɗin kuma an adana su domin ci gaba da binciken kimiyya,” in ji Abubakar.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa bayan cikakken bincike da tantancewa da aka yi a yankin, an ayyana hanyar a matsayin wadda ba ta tattare da barazanar wani bam da aka dasa, wanda hakan ya dawo da tsaro ga masu ababen hawa da mazauna yankin.

Ya kuma buƙaci al’umma su kasance cikin shiri tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

Kungiyoyin ‘yanbindiga suna da sansanoni a cikin wani babban daji da ya ratsa jihohi da dama, ciki har da Zamfara, Katsina, Kaduna, Sokoto, Kebbi, da Neja, inda suke ƙaddamar da hare-hare.