Gwamnatin Ghana ta ba da umarnin a riƙa sarrafa aƙalla kashi 50 cikin 100 na kokon da ake nomawa a cikin ƙasar daga kakar shekarar 2026 da 2027.
Ministan kuɗin Ghana Dakta Cassiel Ato Forson ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin wani taron gaggawa da majalisar zartarwar ƙasar ta yi domin magance matsalolin da fannin noman koko ke fuskanta a ƙasar.
Ministan kuɗin ƙasar ya bayyana cewa majalisar zartarwar ƙasar ta kuma ba da umarnin farfaɗo da muhimman kamanonin gwamnati biyu —kamfanin siyan kayayyaki (PBC) da kamfanin sarrafa koko (CPC) — nan-take.

"Za a farfaɗo da kamfanin ƙasa na saiyan kayayyaki PBC domin ya fara aiki gadan-gadan ya kuma zama kamfanin da ke kan gaba wajen siyan lasisi a fannin koko nan take ," kamar yadda Dakta Ato Forson ya bayyana.
Farfaɗo da kamfanin PBC na zuwa ne a wani muhimmin lokaci inda kamfanonin masu sayen lasisi suke bin kamfanin COCOBOD na gwamnati bashin kimanin sedi biliyan GH¢2.04 , inda wasu manoma ba su samu an biya su ba tun watan Nuwamban shekarar 2025.
Majalisar zartarwar ta kuma ba da umarnin cewa a ware sauran koko na kakar shekarar 2025-2026 domin sarrafawa a cikin gida.
Umarnin zai fara aiki ne nan-take kuma wata alama ce ta jajircewar gwamnatin ƙasar kan sarrafa ababen da ake samarwa a cikin gida da kuma samar da ayyukanyi a fannin koko.















