Dubban ‘yan Venezuela ne ake fargabar cewa sun mutu ranar Alhamis bayan girgizar ƙasa biyu sun yi ta’adi a ciki da kewayen babban birnin ƙasar Caracas, inda mutane suka maƙale ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da suka rufta inda suka haddasa girgiza da yawa daga baya.
Aƙalla mutum 164 aka tabbatar da cewa sun mutu kuma mutum 971 sun ji rauni bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.2 ta afka wa wani wuri da ke da nisan kusan kilomita 160 km (mil 100 ) yamma da Caracas, kuma ƙasa da minti ɗaya bayanta wata gigirzar ƙasa mai ƙarfin maki 7.5 ta auku, in ji Hukumar Binciken Ilimin Ƙasa ta Amurka US Geological Survey).
Shugabar riƙo ta ƙasar Delcy Rodriguez ta tabbatar da adadin waɗanda suka mutun, tana mai gargaɗin cewa adadin zai iya ƙaruwa. Adadi na farko bai haɗa da waɗanda lamarin ya fi shafa ba a jihar La Guaira, kusa da Caracas kuma a nan filin jiragen saman birnin yake, inda bidiyon da shaidu suka ɗauka suka nuna an shiga tashin hankali yayin da rufi ya faɗi ƙasa.
"Gomman gine-gine sun rushe, kuma a halin yanzu muna aiwatar da matakin ƙoƙarin ceto mai ƙarfi domin ceto iya rayukan da Allah Ya ba mu ikon cetowa," in ji ta.
A ƙarshen ranar Laraba, ta ayyana dokar ta ɓaci ta ƙasa bayan girgizar ƙasa biyu masu ƙarfi sun afka wa gaɓar tekun ƙasar da ke arewacin yankin Carribean, lamarin da ya janyo lalata abubuwa da yawa da kuma janyo gargaɗin tsunami da kuma bayar da shawarwari a faɗin yankin .
Ma’aikatan agajin gaggawa sun rinƙa fantsama a kan ɓaraguzan gine-ginen da suka rufta a Caracas da dare, yayin da ‘yanuwa da suka damu suke neman agaji ga ‘yanuwansu da ake fargabar sun maƙale . An tafi da wasu waɗanda aka ceto, wasunsu a kan makara.
"A lokacin da muka suka ƙasan bene, wurin ya yi kama da fim mai ban tsoro," a cewar Maria Alejandra, wata mazauniyar wurin daga wani gini da ke kusa , wadda ba ta ba da sunanta na biyu ba .
"Ya zama mana wajibi mu hau ɓaraguzai da komai da komai. Mai kula da ginin yana tare da jariri kuma dukkan maƙwabtana suna sauƙowa . Amma daga wannan ginin, na gano cewa iyali ɗaya ne kawai ya fito.”
Kazalika Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa girgizar ƙsar guda biyu sun bar "adadin mace-mace masu tayar da hankali," ba tare da ishara ga wani adadi na waɗanda suka mutu a hukumance ba.
"Girgizar ƙasar guda biyu da suka afka wa muhimman mutane na Venezuela suna da ƙarfi sosai kuma sun bar adadidin mace-mace mai tayar da hankali a baya," kamar yadda Trump ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.
"Amurka a shirye take, kuma tana da shirin taimakawa! Na bai wa dukkan hukumomin gwamnatinmu umarnin su shirya domin tafiya da wuri. Za mu kasance a wurin ga manya kuma sabbin abokanmu . Rahotannin farko-farko da ke fitowa ba su da daɗi," in ji shi .

Babbar girgizar kasa
Cibiyar da ke sa ido kan intanet ta NetBlocks ta ba da rahoton cewa an samu katsewar intanet a faɗin yankunan Venezuela, ciki har da babban birnin kasar Caracas, bayan girgizar ƙasar ta lalata wutar lantarki da hanyoyin sadarwa a ƙasar.
Bayanan cibiyar sun nuna yadda aka samu raguwar hanyoyin sadarwa bayan afkuwar tagwayen girgizar ƙasa wadanda suka shafi sassan kayayyakin more rayuwa na ƙasar, kamar yadda NetBlocks ta bayyana a shafinta na X a ranar Alhamis.
Bisa ga sabbin bayanai daga Hukumar Binciken Ilimin Ƙasa ta Amurka (USGS), yankin arewacin Venezuela ya gamu da girgiza mai ƙarfi sakamakon wasu tagwayen girgizar ƙasa masu ƙarfin gaske.
Masana kimiyyar girgizar ƙasa sun tabbatar da cewa girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske da ta kai ƙarfin maki 7.2 ta fara afka wa kusa da gundumar San Felipe, babban birnin jihar Yaracuy.
Sannan bayan daƙiƙa 40, an sake samun wata girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta kai maki 7.5 da ta afka a yankin kudu maso gabashin Yumare.
Babbar girgizar ƙasar ita ce mafi girma da aka taɓa gani a Venezuela sannan mafi ƙarfi a fiye da shekaru 125.
A cewar hukumar USGS, girgizar ƙasar ta kai zurfin kusan kilomita 10 (mil 6.2), inda ta fi muni a yankin yammacin bakin teku na Moron.
Kazalika mummunar girgizar ƙasar ta girgiza babban birnin Caracas sosai, wanda ya haifar da rushewar gine-gine da dama.
Da farko, shugabar rikon kwarya ta kasar, Delcy Rodriguez ta tabbatar da lalacewar hanyoyin sufuri na yankin, inda ta ce an rufe filin jirgin saman Simon Bolivar da ke Maiquetia saboda mummunar lalacewar kayayyakin more rayuwa da aka samu a tashar da kuma hanyoyin tashi da saukar jiragen sama.
A halin da ake ciki, hukumomin tsaro na farar-hula suna ci gaba da tura jami’an agaji zuwa yankunan da abin ya fi shafa don tantance yawan barnan da ifti’la’in ya haifar.
Bidiyoyi da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ƙura mai kauri ta lullube sassan kasuwanci a babban birnin kasar yayin da gine-ginen suka zama baraguzai.
Ma'aikatan gaggawa suna aikin bincike kan tarkacen don gano 'yan ƙasar da suka makale ko kuma suka ji rauni.
'Yanayi mai tayar da hankali'
Ministan Cikin Gida na Venezuela, Diosdado Cabello, ya tabbatar wa kafafen yada labarai na cikin gida cewa mummunar girgizar kasar ta haifar da lalacewar tsarin gine-gine, wanda ya yi sanadiyyar rushewar gidaje da manyan gine-gine.
“Dukkan hukumomin tsaro da na agajin gaggawa, gami da jami’an kariya na farar-hula, da masu sa-kai, da jami’an kashe gobara, da kuma ‘yan sanda, an tura su baki daya zuwa wurin da abin ya faru,” in ji Cabello yayin wani shiri kai-tsaye a gidan talabijin na gwamnati.
Ministan ya bayyana cewa akwai wani “yanayi mai tada hankali” musamman a unguwar Altamira da ke Caracas, inda bangaren dogayen gine-gine da mutane ke zaune suka ruguje, wanda hakan ya sa aka iya ganin kayayyakin daki tun daga kan titi. Cabello ya yi kira ga mazauna yankunan biranen da abin ya shafa da su fito waje, su guji zama a cikin gidaje, domin kauce wa asarar rayuka daga motsin kasa da ka iya biyo bayan girgizar.
“Muna ba ku shawarar ku ci gaba da zama a tituna, ku kula da yara da tsofaffi, sannan ku yi kokarin kwantar da hankalinku yayin da ake gudanar da tsare-tsaren ceto,” in ji shi.
A daidai lokacin da ake fama da karuwar rugujewar gine-gine da kuma katsewar wutar lantarki a wasu yankuna, Rodriguez ta mika godiya ga Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyoyin kasa da kasa, da gwamnatocin kasashen waje daban-daban saboda nuna juyayi da kuma tayin tallafin jinkai.
Musamman ta gode wa Colombia, da Brazil, da Mexico, da Turkiyya, da Jordan, da Barbados, Curacao da kuma Birtaniya saboda tayin tallafinsu wajen gudanar da bincike da ceto mutane daga gine-ginen da suka rushe.
Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, shi ma ya ce ya umarci Ma’aikatar Harkokin Wajen kasarsa da ta auna halin da ake ciki a kasar da kuma matakan tallafi da Brazil za ta iya bayarwa.
“Na samu labari, cikin kaduwa da matukar damuwa, game da illolin da girgizar kasar da ta afka wa Venezuela a wannan Larabar ta haifar,” in ji Lula a shafinsa na X.
Lula ya sake jaddada aniyar Brazil ta mara wa gwamnatin riko ta Shugaba Delcy Rodriguez baya wajen farfado da yankunan da abin ya shafa na "wannan kasa ta 'yan’uwa."
Cibiyar Gargadin Tsunami ta Pacific (PTWC) ta fitar da gargadin barazanar tsunami a gabar tekun Venezuela da ke kusa, da kuma makwabtan tsibiran Aruba, Bonaire, da Curacao.
An fara aiki da tsarin fadakarwa game da tsunami ga kasashen Puerto Rico da Tsibiran Virgin Islands na Amurka, yayin da hukumomi ke sanya ido sosai kan ma’aunan igiyar ruwa na gabar teku domin gano duk wani motsi na daban na torokon teku.











