| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci a soke shirin gyaran hali na tubabbun 'yan Boko Haram
Shirin gwamnatin Nijeriya na gyaran hali da kuma sake mayar da ‘yanta’adda da suka tuba cikin al’umma ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka yi ta jawo ce-ce-ku-ce kan dabarun yaƙi da ta'addanci mafi rikitarwa a Nijeriya.
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci a soke shirin gyaran hali na tubabbun 'yan Boko Haram
Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi kira da a kawo karshen shirin gyaran hali da kuma sake mayar da tubabbun mambobin kungiyar Boko Haram cikin al’umma / TRT Afrika Hausa

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ƙasar da ta kawo ƙarshen shirin gyaran hali da sake mayar da tubabbun mambobin ƙungiyar Boko Haram cikin al’umma, tana mai bayyana shirin a matsayin wanda ba shi da wani amfani ganin yadda ake fama da taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.

Ƙudurin ya biyo bayan wata zazzafar muhawara da ta taso sakamakon mutuwar da tsohon kakakin rundunar sojin Nijeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) da wasu manyan jami’an soji suka yi a hannun ‘yanbindiga a ƙasar.

A yayin da suke tafka muhawara kan ƙudurin dokar, wanda Sanata Abdul’Aziz YarAdua, Sanatocin sun ce duk da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na ganin ta ja tubabbun ‘yan Boko Haram a jiki ta hanyar saka su cikin al’umma, amma ba a daina kai hare-haren ta’addanci a arewa maso gabashin ƙasar ba.

Sanata Joseph Ikpea, wanda ya jagoranci kira kan soke shirin sake mayar da tubabbun mambobin ƙungiyar Boko Haram cikin al’umma, ya ce bai yi wani amfani ba tun da a baya bayan nan ana samun ƙaruwar hare-haren ‘yanta’addan na Boko Haram a Nijeriya.

Sanatoci da dama, ciki har da Adams Oshiomhole, sun bayyana cewa yafewa da kuma gyara halin tsoffin ‘yan Boko Haram ɗin  “ba su da ma’ana” a halin da Nijeriya ke ciki, inda suka yi kira da a yi dokar da za ta kawar da shirin.

‘Yanmajalisar sun kuma yanke shawarar ganawa da Shugaba Bola Tinubu don tattauna kan batun da ma wasu batutuwa na rashin tsaro a Nijeriya.

An ƙaddamar da shirin ne, wanda aka fi sani da Operation Safe Corridor, a shekarar 2016 a zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari don kawar da tsattsauran ra’ayi da gyara hali da kuma sake mayar da tubabbun ‘yan Boko Haram cikin al’umma.

Wasu jihohi na yankin na Arewa maso Gabas, ciki har da jihar Borno, inda rikicin Boko Haram ya samo asali, sun rungumi shirin sake shigar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’umma.

Bayanai sun nuna cewa ya zuwa watan Yunin shekarar nan ta 2026, tubabbun ‘yan Boko Haram 9,680 ne suka ci moriyar shirin.

Sai dai shirin ya yi ta jawo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin ba zai yi wani tasiri ba wajen kawar da rikicin Boko Haram, wanda aka fi alaƙantawa da na aƙida.

Kazalika, masu suka sun nuna damuwa kan yadda, a cewarsu, gwamnatoci suka fi nuna damuwa kan gyara halin tubabbun mayaƙan Boko Haram maimakon iyali da ‘yan’uwan waɗanda rikicin ya shafa.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dubban ɗaruruwan mutane ne suka mutu sakamakon rikicin Boko Haram, wanda aka soma a shekarar 2009, kana rikicin ya raba miliyoyin jama’a da muhallansu a yankin Tafkin Chadi, musamman a Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.