| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Bincike: Amincewar duniya ga Netanyahu ta yi ƙasa, martabar Isra'ila na ci gaba da urƙushewa
Sakamakon binciken ya nuna cewa a mafi yawan ƙasashen da aka gudanar da shi, rinjayen jama'a sun ce ba su da tabbacin cewa Netanyahu zai yi abin da ya dace a harkokin duniya.
Bincike: Amincewar duniya ga Netanyahu ta yi ƙasa, martabar Isra'ila na ci gaba da urƙushewa
Bincike: Amincewar Duniya ga Netanyahu Ta Yi Ƙasa, Martabar Isra'ila Na Ci Gaba da Durƙushewa / Reuters

Wani sabon binciken ra'ayin jama'a da cibiyar bincike ta Pew Research Center ta gudanar a ƙasashe 36 na duniya ya nuna cewa mafi yawan mutane ba su da ƙwarin gwiwa ga Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, yayin da martabar ƙasar Isra'ila ke ci gaba da fuskantar koma baya a idon al'ummar duniya.

Binciken, wanda aka gudanar tsakanin 8 ga Fabrairu zuwa 12 ga Mayu, 2026, ya nuna cewa matsakaicin kashi 67 cikin 100 na waɗanda aka tambaya suna kallon Isra'ila da mummunan ra'ayi, yayin da kashi 25 cikin 100 kawai suka bayyana cewa suna da kyakkyawan ra'ayi game da ƙasar.

Sakamakon binciken ya nuna cewa a mafi yawan ƙasashen da aka gudanar da shi, rinjayen jama'a sun ce ba su da tabbacin cewa Netanyahu zai yi abin da ya dace a harkokin duniya.

Ƙasashen da suka fi nuna rashin amincewa da shi sun haɗa da Turkiyya inda kashi 95 cikin 100 suka ce ba su da ƙwarin gwiwa a kansa, yayin da kashi 1 cikin 100 kacal suka nuna amincewa.

A Malaysia da Pakistan ma, kashi 89 da 88 cikin 100 bi da bi sun bayyana rashin amincewa da shugaban na Isra'ila.

Haka kuma ƙasashe kamar Sweden, Japan, Faransa, Birtaniya, Australia, Jamus da Netherlands sun nuna babban matakin rashin amincewa da shi.

Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka

A Nijeriya, binciken ya nuna cewa kashi 45 cikin 100 na waɗanda aka tambaya ba su da ƙwarin gwiwa ga Netanyahu, yayin da kashi 43 cikin 100 suka ce suna da ƙwarin gwiwa a kansa.

A Kenya kuwa, kashi 56 cikin 100 sun nuna amincewa da shi, yayin da kashi 39 cikin 100 suka ce ba su amince da shi ba. A Ghana kuma, masu amincewa da shi da waɗanda ba su amince da shi ba sun yi kunnen doki da kashi 38 cikin 100 kowanne.

Yaƙin Gaza na tasiri kan ra'ayin jama'a

Masu nazari na ganin cewa sakamakon binciken na da alaƙa da yadda duniya ke kallon yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya da suka ƙara tsananta a watannin baya-bayan nan.

Haka kuma hare-haren da Isra'ila ta kai a yankuna daban-daban da kuma rikicin da ya shafi Iran sun ƙara jawo muhawara da suka sauya yadda mutane da dama ke kallon Isra'ila da shugabancinta.

Martabar Isra'ila Na Fuskantar Kalubale

Binciken ya nuna cewa ba wai amincewar jama'a ga Netanyahu ce kawai ta ragu ba, har ma da yadda ake kallon Isra'ila gaba ɗaya. A mafi yawan ƙasashen da aka gudanar da binciken, adadin masu kallon Isra'ila da mummunan ra'ayi ya fi nesa da adadin masu kallonta da kyau.

Wannan na nuna irin ƙalubalen da Isra'ila da shugabanninta ke fuskanta wajen inganta martabarsu a idon al'ummar duniya a daidai lokacin da rikice-rikicen yankin ke ci gaba da janyo hankalin duniya baki ɗaya.