Turkiyya ta ce a shirye take domin taimakawa wurin sake gina Ukraine

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Omer Bolat ya ce a shirye Ankara take domin aikawa da ƙwararun 'yan kwangila na Turkiyya waɗanda suka san makamar aiki zuwa Ukraine domin sake gina ta.

Haka kuma Bolat ya samu tarba daga firaministan kasar Ukraine Denys Shmyhal, inda suka tattauna kan matakan da za su ɗauka na kara ciyar da huldar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Turkiyya da Ukraine gaba. / AA

Turkiyya ta ce a shirye take ta taimaka wa Ukraine wurin sake gina ƙasar da kuma faɗaɗa cikikayya da kasuwancin ƙasar, kamar yadda Ministan Kasuwanci na Turkiyya Omer Bolat ya bayyana.

Bolat ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara Kiev babban birnin na Ukraine tare da rakiyar wata tawaga wadda ta haɗa da ‘yan kwangilar Turkiyya.

“A lokacin ziyararmu zuwa Ukraine, Shugaban Ukraine Mista Volodymyr Zelenskyy ya karɓe mu, tare da ‘yan kwangilar Turkiyya waɗanda suka raka mu,” kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X a ranar Alhamis.

A lokacin tattaunawar, an tattauna kan batun dangantakar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin Turkiyya da Ukraine da kuma neman hanya mai ɓullewa ga ƙasashen a nan gaba.

 “Mun jaddada aniyarmu ta gudanar da kasuwanci wanda ya kai dala biliyan 10, wanda lamari ne Mista Zelenskyy ya kudurta tare da shugaban ƙasarmu, za mu aiwatar da shirinmu na yarjejeniyar kasuwanci maras shinge, kuma a shirye muke mu aika ƙwararrun ‘yan kwangilarmu na Turkiyya waɗanda suka san makamar aiki ga Ukraine domin sake gina ƙasar da gudanar da ayyuka,” in ji shi.

“Bisa wannan, ina so na yi godiya ga Mista Zelenskyy kan goyon bayan da ya bayar da gudanar da taron farko wannan kwamiti na musamman wanda zai taka rawa wurin sake gina Ukraine, a Kiev.”

Haka kuma Bolat ya samu tarba daga firaministan kasar Ukraine Denys Shmyhal, inda suka tattauna kan matakan da za su ɗauka na kara ciyar da huldar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Turkiyya da Ukraine gaba.

"Bugu da kari, mun sake jaddada goyon bayanmu a matsayinmu na Turkiyya don tabbatar da yankin Ukraine da 'yancin kai da kuma ƙarfin iko, tare da jawo hankali kan muhimmancin tattaunawa don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinmu," in ji Bolat.