| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Turkiyya da Saudiyya da Masar da wasu ƙasashe biyar sun yi gargaɗin cewa matakan Isra'ila a wurare masu tsarki na Musulunci da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye suna ruruta wutar tashin hankali da kuma barazana ga damar zaman lafiya.
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
(TOSHON HOTO) Musulmai suna Sallah a Masallacin Ƙudus bayan Isra'ila ta sake buɗe haraar masallacin bayan 41 da rufe shi a gabashin birnin Ƙudus . / AA Archive

Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya da ƙasashen Musulmi bakwai sun yi Allah wadai da abin da suka kira keta alfarmar matsayi na tarihi da kuma shari’a na Birnin Ƙudus da Isra’ila ke yi a wurare masu tsarki na Musulunci da Kiristanci, inda suka fi nuna damuwa kan Masallacin Ƙudus da kuma Al-Haram Al-Sharif.

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa ranar Alhamis, ministocin harkokin wajen Turkiyya da Masar da Indonesia da Jordan da Pakistan da Qatar da Saudiyya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun yi tir da kutsawa da Yahudawa ‘yankama-wuri-zauna na Isra’ila da jami’anta ke yi cikin harabar masallacin a ƙarƙashin kariyar ‘yansanda tare da ɗaga tutar Isra’ila a cikin harabar.

Sun bayyana matakan a matsayin tsagoron keta dokar jinƙai ta ƙasa da ƙasa, suna masu gargaɗin cewa ta kasance wata tsokana ga Musulman duniya wadda ba za a lamunta ba.

Ministocin sun ce irin waɗannan matakan sun keta alfarmar Birnin Ƙudus da kuma yin zagon-ƙasa ga ƙoƙarin kiyaye zaman lafiya a ɗaya daga cikin wuraren addini da na tashin hankalin siyasa da ya yi jan hankali a duniya.

Dole matsayar Masallacin Ƙudus ta sauya

Sanarwar ta tabbatar da yin watsi da duk wani ƙoƙari na sauya matsaya ta tarihi da ta shari’a ta wurare masu alfarma na Musulmi da na Kirista a Birnin Ƙudus.

Minsitocin sun jaddada cewa harabar Masallacin Ƙudus gabaɗaya — wanda ya kai dunam 144 — wuri ne na ibada ga Musulmai kaɗai.

Sun kuma jaddada muhimmiyar matsaya ta Masarautar Hashimawa ta Jordan a matsayar mai kula da shi kuma sun bayyana cewa gidauniyar Birnin Ƙudus da ɓangaren gudanarwa na Masallacin Ƙudus mai alaƙa da ma’aikatar gidauniya ta Jordan, ta kasance hukuma ɗaya tilo mai alhakin gudanar da wurin da kuma ba da izinin shige da fice daga wurin.

Sun yi watsi da duka wani ƙoƙarin Isra’ila na nuna iko kan wuraren Falasɗinawa da ta mamaye ciki har da gabashin Birnin Ƙudus.

Suka ga ‘yan mamaya da tashin hankali

Ministocin sun kuma yi Allah wadai da izinin da Isra’ila ta bayar ga sabbin unguwanni 30, tana mai bayyana matakin a matsayin mummunar keta dokar ƙasa da ƙasa da Ƙudirin Majalsair Ɗinkin Duniya da kuma ra’ayi na shawara da kotun hukunta manyan laifuka na shekarar 2024.

Sun yi gargaɗin cewa faɗaɗa unguwannin ‘yan-kama-wuri-zauna da kuma ƙaruwar hare-harensu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye —musamman hare-hare kan makarantun Falasɗinawa da ƙananan yara —suna zagon ƙasa kai-tsaye ga yiwuwar kafa ƙasar Falasɗinawa nan gaba.

Sanarwar ta yi kira da a bayyana gaskiya game da hare-haren ‘yan-kama-wuri-zauna, kuma ta yi tir da ko wane ƙoƙari na ƙwace ƙasar Falasɗinawa ko kuma korar Falasɗinawa ala tilas.

Sun ce irin waɗannan matakan daidai suke da kai hari kan mafita ta ƙasashe biyu masu cin gashin kansu kuma suna barazana ga zaman lafiya na yanki ta hanyar ƙara tashin hankali da kuma raunata ƙoƙarin diflomasiyya.

Kira ga mataki na ƙasa da ƙasa

Ministocin sun yi kira ga ƙasashen duniya su ɗauki “matakai bayyanannu masu ƙarfi ” domin dakatar da keta alfarma na Isra’ila da kuma tabbatar da sauke nauyi na shari’a da na sanin ya kamata.

Sun yi kira ga sabunta ƙoƙari na ƙaddamar da cikakkiyar mafita ta siyasa bisa kafa ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta bisa kan iyakoki na 4 ga watan Yunin shekarar 1967, inda Gabashin Birnin Ƙudus zai kasance babban birninta.

Ƙungiyar ta tabbatar da goyon baya mai ƙarfi ga ‘yancin zaɓar makoma ta Falasɗinawa kuma ta yi gargaɗin cewa ci-gaba da rashin ɗaukar mataki zai ƙarfafa rashin zaman lafiya ne kawai a yankin.