Haaland ya kama hanyar kamo Messi da Ronaldo wajen cin ƙwallaye

Erling Haaland na Norway ya ci gaba da cirar tuta wajen zura ƙwallaye, inda yake ƙare shekarar nan a sahun gaba a gasar Firimiya da yake bugawa tsawon shekara uku yanzu.

By
Erling Haaland na da shakru 25 ne kuma ɗan asalin Norway ne. / AP

Tauraron ɗanwasan Manchester City, Erling Haaland ya kama hanyar shiga sahun gwarazan ‘yanwasan ƙwallo a tarihi, wajen cin ƙwallaye da ajiye tarihi a ƙungiyoyi da gasannin da suka buga.

Tuntuni ake ganin Haaland a matsayin mai nasibin da zai iya kamo zaƙaƙuran ƙwallo irin su Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a fannin zura ƙwallo.

Messi ɗan asalin Argentine da Ronaldo ɗan asalin Portugal sun daɗe suna mamaye muhawarar mafi shaharar ɗanƙwallon wajen nuna bajinta a tarihin ƙwallo, tsawon sama da shekaru 20.

Zuwa ƙarshen 2025, Haaland ya ci ƙwallo da ba da taimakon cin ƙwallo da ya kai jimillar 405 bayan buga jimillar wasanni 403, ga tawagar ƙasarsa da kuma ƙungiyoyin da ya bugawa.

Sai dai matashin ɗanwasan ɗan asalin Norway, Haaland ya sha nisanta kansa daga kwatanci da Ronaldo ko Messi, ganin tarin nasarorin da suka samu a rayuwarsu ta ƙwallo.

Kamo hanya

Ko da aka taɓa tambayar Haaland ko ya damu da ya kamo Messi da Ronaldo, sai ya ka da baki ya ce, “A’a, sam a’a, nesa da haka. Babu wanda zai iya kusantar su, don haka ni ma a’a.”

Amma fa ko a zallar zura ƙwallaye, Ronaldo na da jimillar ƙwallo 954, inda Messi ke biye masa da ƙwallo 896. Hakan na nufin akwai aiki a gaban Haaland mai ƙwallo 267 daga wasanni 322.

A dunƙule, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun ci kambin gwarzon ɗanƙwallon duniya na Ballon d’Or sau 13, inda Messi ya ci sau 8, Ronaldo ya ci sau biyar.

A halin yanzu dai, a kakar bara Ronaldo ya ci kyautar yawan cin ƙwallaye a karo na biyu a Al Nassr ta Saudiyya. Shi ma Messi ya ci irin wannan kyautar a 2025.

Ronaldo ya ci ƙwallo da ba da tallafin ƙwallo 143 cikin wasanni 226 ga ƙasarsa Portugal. Messi ya ci ƙwallo da tallafin ƙwallo 172 daga wasanni 193 ga ƙasarsa Argentina.

A ɓangaren Haaland, ya zamo wanda ya fi cin ƙwallaye a gasar Firimiya ta Ingila a shekaru biyu cikin ukun da ya kwashe a Manchester City.

A bana ma tuni yake kangaba a cin ƙwallo da ƙwallaye 17. Sannan kuma a tawagar ƙasarsa Norway ya ci ƙwallo 36 daga wasanni 27.