Sabon Jagoran Addini na Iran Mojtaba Khamenei yana nan "lafiya kalau" duk da rahotannin cewa ya ji rauni a lokacin yaƙin da ke gudana tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka, in ji ɗan shugaban ƙasar Iran a ranar Laraba.
"Na ji labarin cewa Mista Mojtaba Khamenei ya ji rauni. Na tambayi wasu abokai da suke da alaƙa da shi. Sun gaya mini cewa, godiya ta tabbata ga Allah, yana nan lafiya kalau," in ji Yousef Pezeshkian, wanda shi ma mai ba da shawara ga gwamnati ne, a cikin wani rubutu a shafinsa na Telegram.
Gidan talabijin na gwamnati ya kira Khamenei "jarumin yaƙin Ramadan da ya ji rauni" amma bai fayyace irin raunukan da aka samu ba.
A baya, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai yi imani sabon shugaban ƙoli na Iran Mojtaba Khamenei zai iya zaman lafiya da Amurka ba, yana ƙara ƙarfafa sukarsa ga shugabancin Tehran a yayin rikicin da ke ci gaba.
"Ba na jin zai iya rayuwa cikin salama," in ji Trump a wata hira da Fox News da aka watsa, inda ya ƙara da cewa bai ji daɗin wannan shawarar ta Iran ba.
Trump ya taɓa kiran nadin Khamenei "babban kuskure," yana gargadi cewa sabon shugaba "ba zai daɗe ba" ba tare da amincewar Amurka ba.
Sabon jagoran addinin ɗa ne kuma magajin tsohon jagoran addinin na Iran Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren Amurka da Isra'ila a Iran a ranar 28 ga Fabrairu, abin da ya janyo yaƙi a fadin Gabas ta Tsakiya.
Mojtaba Khamenei, mai shekaru 56, mutum ne wanda bai faye fiotwa a bainar jama'a ko magana a tarukan hukuma ba, har yanzu bai yi magana da ƙasa ko fitar da wata sanarwa ba tun lokacin da aka bayyana shi a matsayin jagoran addini a ranar Lahadi.
A cikin wani rahoto na ranar Laraba, New York Times, tana ambaton jami'ai uku na Iran ba tare da sunaye ba, ta ce Khamenei "ya ji rauni, ciki har da ƙafafunsa, amma a ankare yake kuma yana ɓuya a wani wuri mai matuƙar tsaro tare da iyakantaccen sadarwa."
















