| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Infantino ya ce FIFA ta fasa shirin sayar da hannayen-jari na Kofin Duniya ga ‘yan kasuwa
Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Duniya FIFA ta soke shirinta na bai wa 'yankasuwa damar su zuba jari a muhimman shirye-shiryenta bayan zazzafar martani daga jami'an ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.
Infantino ya ce FIFA ta fasa shirin sayar da hannayen-jari na Kofin Duniya ga ‘yan kasuwa
Zane ya nuna hoton inuwar Gianni Infantino, shugaban FIFA, da lambobi "20%" da kuma zanen tashin hannayen jari

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA Gianni Infantino ya ce hukumar ta soke shirin sayar da hannayen-jari na Kofin Duniya ga ‘yan kasuwa bayan zazzafar martani.

"Bayan na saurari dukkan ra’ayoyi a hankali, ya bayyana a gare ni cewa shirin ya haifar da wani irin rarrabauwar kai wanda, ko ma wane irin goyon baya [aka samu], ba zai taimaka wa burin da aka ayyana tun daga farko ba," kamar yadda Infantino ya bayyana ranar Jumma’a.

"A ko da yaushe manufarmu ta kasancewa — kuma za ta ci gaba da kasancewa — a haɗa kai da inganta [abubuwa]," kamar yadda Shugaban FIFA Gianni Infantino ya bayyana a wata sanarwa.

"Sakamakon haka, wannan shawarar ba za ta ci gaba ba."

A ranar Talata, FIFA ta ce tana shirin kafa wani ƙaramin kamfani na $20bn a ƙarƙashinta wanda zai ringa jagorantar Gasar Kofin Duniya da sauran gasarta, inda za ta sayar da har kashi 20 cikin 100 na hannayen jari ga masu zuba jari daga wajen hukumar. Sayar da hannayen jarin zai samar da abin da ya kai dala biliyan 4.2.

Adawa ga shirin FIFA

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ƙasashen Turai UEFA da dukkan hukumommin ƙwallon ƙafar ƙasashe 55 na Turai sun yi watsi da shawarar kuma sun yi barazanar ƙaurace wa duk wata gasar FIFA idan ba ta yi watsi da shirin ba.

Kazalika Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Arewaci da Tsakiyar Amurka da kuma yankin Karibiyan (CONCACAF) da hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe 41 da ke cikinta su ma sun yi watsi da ita, suna ishara ga tsaga gaskiya da jagoranci da kuma rashin tuntuɓa yadda ya dace.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta nahiyar Asiya, wadda ke wakiltar hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe 47, ta shiga cikin adawar UEFA da Concacaf . Tare, hukumomi ukun suna wakiltar mambobi 143 daga cikin ƙasashe 211 mambobin FIFA.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) saura ƙiris ta yi watsi da shawarar kuma ta ce za ta yi nazari a kan shirin a wani zaman kwamitin zartarwa a mako mai zuwa.

Kazalika hukumar ƙwallon ƙafa ta Oceania (OFC) ita ma ta ce za ta tattauna batun a zamanta na zartarwa na watan August.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta kudancin Amurka CONMEBOL ta ce ta ƙaddamar da tuntuɓa da mambobinta hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe goma kuma ta kira wani zama na sake nazari a kan batun.

Adawa ga batun ya fita daga cikin hukumomin ƙwallon ƙafa zuwa waje.