Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Ministocin sun tattauna ne kan yadda za a yayyafa ruwa kan wutar da ke ruruwa a yankin a daidai lokacin da ake tsoron harin Amurka kan Tehran.
Ministan Harkokin Waje na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan, ya yi tattaunawa da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar don tattaunawa kan yadda za a yayyafa ruwa kan wutar da ke ruruwa a yankin a daidai lokacin da ake tsoron harin Amurka kan Tehran.
A cewar wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Waje, a ranar Alhamis ta fitar, bin Farhan ya yi magana ta waya da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi don tattauna abubuwan da ke faruwa a yankin da hanyoyin da za a inganta tsaro da kwanciyar hankali.
Ministan Harkokin Wajen Saudiyya da takwaransa na Oman, Badr Albusaidi, sun kuma yi bita ta waya kan abubuwan da ke faruwa a yankin da kokarin hadin gwiwa da nufin samar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin yankin, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar SPA.
Bin Farhan da Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Waje Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani sun tattauna kan kokarin inganta tsaro da kwanciyar hankali a yankin, in ji SPA.
Trump ya sassauta magana kan Iran
Wannan kai ziyara ta diflomasiyya ta biyo bayan yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya sassauta maganganu kan Iran a jawabin da ya yi a Fadar White House a ranar Laraba da dare.
Trump ya ce an sanar da shi cewa an dakatar da hukuncin kisa a Iran, amma ya yi gargaɗi cewa "idan wani abu makamancin haka ya faru, za mu ji baƙin ciki gaba ɗaya."
Tsoron yiwuwar harin Amurka kan Iran ya karu a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, inda ake zanga-zangar adawa da gwamnati ƙasar tun karshen watan da ya gabata saboda tabarbarewar halin tattalin arziki a ƙasar.
A ranar Laraba, gidan rediyon gwamnati na Isra’ila ya ruwaito cewa nazarin Isra’ila ya nuna cewa Amurka na iya kai hari cikin Iran a cikin kwanakin da ke tafe.
Jami’an gwamnatin Iran sun zargi Amurka da Isra’ila da goyon bayan abin da suka bayyana a matsayin "hargitsi" da "ta'addanci" a tsakiyar zanga-zangar da ke gudana.
Hukumomin Iran ba su fitar da ainahin ƙididdigar wadanda suka mutu ko wadanda suka mutu da waɗanda aka tsare ba. Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam mai hedkwata a Amurka ta kiyasta cewa fiye da mutum 2,600 ne suka rasa rayukansu, ciki har da masu zanga-zanga da jami’an tsaro.