Yawan masu kamuwa da cutar kansa a duniya na iya kaiwa kusan miliyan 35 a duk shekara nan da shekarar 2050, matuƙar gwamnatoci ba su ɗauki matakan gaggawa na ƙarfafa rigakafi, faɗaɗa samun kulawar lafiya, da rage gibin da ke akwai wajen samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya ba, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
A cikin rahotonta na Global Status Report on Cancer 2026, wanda ta fitar tare da Hukumar Bincike kan Cutar Kansa ta Duniya (International Agency for Research on Cancer), WHO ta ce cutar kansa ita ce ta biyu cikin manyan musabbabin mutuwa a duniya bayan cututtukan zuciya da hanyoyin jini, inda take kashe kimanin mutane miliyan 10 a kowace shekara, wato sama da mutum 26,000 a kullum.
Rahoton ya kuma yi gargaɗin cewa gibin da ke akwai wajen kula da masu cutar kansa na ƙara faɗaɗa, saboda damar samun rigakafi, gano cutar da wuri, magani da kuma kulawar bayan magani na bambanta ƙwarai tsakanin ƙasashe.
Haka kuma, yawan masu rayuwa bayan kamuwa da cutar ya fi ƙanƙanta a ƙasashe masu ƙarancin kuɗaɗen shiga idan aka kwatanta da ƙasashe masu arziki.
WHO ta ce cutar kansa na shafar kusan kowa da kowa, inda aka yi hasashen cewa kashi 92 cikin 100 na mutane za su taɓa fuskantar cutar a rayuwarsu, ko dai su kansu su kamu da ita ko kuma wani na kusa da su a cikin iyali.
"Damar mutum ta tsira daga cutar kansa bai kamata ta dogara da inda aka haife shi ko kuma yawan kuɗin da yake samu ba," in ji Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus.
















