'Yanwasan Masar sun mara wa Salah baya kan matsalarsa da Liverpool
An cire sunan Mohamed Salah daga jerin 'yanwasan da suka kara da Inter Milan a wasan gasar Zakarun Turai da aka yi ranar Talata nana.
Yayin da makomar Mohamed Salah a Liverpool take cikin reto, 'yanwasan tawagar ƙasarsa Masar sun nuna goyon bayan ga kyaftin ɗinsu gabanin Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta 2025 AFCON da za a fara a Morocco.
Tawagar Masar, wadda ta taɓa lashe kofin AFCON sau bakwai tana cikin Rukunin B tare da Angola, Afirka ta Kudu, da Zimbabwe, kuma za su yi sansani a Morocco a garin bakin teku na Agadir.
"Yan wasa irin shi ba a ajiye su a benci," in ji ɗanwasan gaban Masar, Ahmed "Kouka" Hassan a shafinsa na sada zumunta, da yake sharhi kan ajiye Salah a benci a wasanni ukun na baya-bayan nan na Liverpool, inda sau ɗaya kacal aka saka shi.
"Idan za a bar shi a benci, to dole ne ku tabbatar shi ne na farko da za a saka yayin canji, bayan minti 60, ko minti 65 idan an tsawaita."
"Mo ba kawai abokin wasa ba ne, shi ne jagora, abin-koyi ga kulob da ƙasa. Ci gaba da aiki tuƙuru ɗan-uwana, kowane hali a rayuwa na mai wucewa ne, irin waɗannan lokutan suna wucewa, abin da zai tabbata shi ne girmanka."
Juriya da ƙarko
Kocin tawagar Masar ƙungiyar, kuma tsohon tauraron ɗanwasa, Hossam Hassan ya wallafa hotonsa tare da Salah haɗe da saƙon: "Koyaushe kai alama ce ta juriya da ƙarko."
"Gwarzon Liverpool mafi girma a tarihi," in ji ɗanwasan gefe, Ahmed "Zizo" El Sayed.
Shi ma mai tsaron ragar Masar, Mohamed Sobhy ya kira Salah da cewa, "ko da yaushe kai ne mafi kyau".
Liverpool na fafutukar kare kambin Firimiya a kakar bana, kuma suna matsayi na 10 bayan buga wasanni 15. Maki 10 Arsenal da ke kangaba a teburi.
Shi kansa Salah yana fuskantar ƙalubale, inda zuwa yanzu ya zura ƙwallaye huɗu kacal bayan buga wasanni 13.
Bayan kammala wasan da Liverpool ta yi canjaras 3-3 da Leeds United a ranar Asabar da ta gabata, Salah ya shaida wa 'yan-jarida cewa, "Da alama kulob ɗina yana so ya ɗora min laifin... akwai wanda bai so in kasance a kulob ɗin."
A gasar AFCON da za a fara ranar 21 ga Disamba, Masar na da yalwar 'yanwasan gaba kamar Salah, Omar Marmoush na Manchester City, Mostafa Mohamed na Nantes, Mahmoud 'Trezeguet' Hassan, da Zizo daga manyan kungiyar Al Ahly na Cairo.