27 Fabrairu 2026
Jirgin ruwan Amurka mai filin jirgin sama mai suna Gerald R Ford, wanda shi ne irinsa mafi girma a duniya, ya isa gaɓar tekun Isra'ila a ranar Juma'a, a cewar tashar Isra'ila ta Channel 12.
Babu wata sanarwa a hukumance da sojojin Amurka suka fitar dangane da wannan lamari.
Rahotannin kafafen watsa labarai sun nuna cewa isowar wannan jirgin ya biyo bayan saukar jiragen tankin mai guda 20 na Amurka a Isra'ila a ranar Alhamis da dare.
ZA KU SO WAƊANNAN
Hukumar Watsa Labarai ta Isra'ila a baya ta sanar da isowar jiragen tankin mai huɗu samfurin US KC-46A Pegasus a filin jirgin saman Ben Gurion da ke kusa da Tel Aviv.
Rahotannin sun ce zuwan waɗannan jiragen wani ɓangare ne na ƙarin ƙarfin soji na Amurka a yankin, saboda yiwuwar kai hari na soja kan Iran.














