| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe manoma 17 a Jihar Zamfarar Nijeriya
Kungiyoyin 'yan bindiga da suka ƙware wajen satar mutane domin neman kudin fansa da kuma satar shanu suna addabar al'ummomi a arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda suke kai hare-hare masu muni tare da ƙaƙaba haraji ga manoman da ke son zuwa gonakinsu.
'Yanbindiga sun kashe manoma 17 a Jihar Zamfarar Nijeriya
Ana yawan fama da matsalar tsaro a arewacin Nijeriya / Reuters

'Yanbindiga sun kashe manoma 17 a arewa maso yammacin Nijeriya a ranar Jumma'a a wani sabon harin da aka kai wa manoma tun bayan fara kakar noma, kamar yadda wani jami'in yanki da mazauna wurin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Kungiyoyin 'yan bindiga da suka ƙware wajen satar mutane domin neman kudin fansa da kuma satar shanu suna addabar al'ummomi a arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda suke kai hare-hare masu muni tare da ƙaƙaba haraji ga manoman da ke son zuwa gonakinsu.

Majiyoyi sun ce 'yanbindigar da suka je a kan babura, sun je ne a matsayin baƙi, inda daga baya suka buɗe wa manoma wuta yayin da suke aiki a gonakinsu a ƙauyen Goron Namaye da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum 17 tare da raunata wasu biyar.

"Na samu rahoton kashe mutane 17 a al'ummar Goron Namaye da safiyar yau," in ji Sanusi Dosara, shugaban gudanarwa na yankin Maradun.

Dosara ya bayyana yawaitar hare-haren da ake kai wa manoma a fadin Jihar Zamfara a matsayin "munanan ayyuka da ke da nufin kawo cikas ga ayyukan noma na shekarar 2026."

"Mun binne mutane 17 da aka kashe a harin," in ji Abubakar Jarra, wani shugaban al'umma a ƙauyen, yana mai ƙarawa da cewa wasu biyar sun jikkata, uku daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.

"Muna kira ga hukumomi da su tura jami'an tsaro domin kare manomanmu."

Mansir Muhammad, wani mazaunin Goron Namaye wanda ya tabbatar da adadin wadanda aka kashe, ya ce maharan sun shigo ne a matsayin baƙi tare da boye makamansu, sannan suka fito da su bayan sun isa kusa da manoman.

A cewar Nura Musa, wani mazaunin yankin,  ya ce harin na iya kasancewa ramuwar gayya ce kan kashe 'yanbindiga 13 da jami'an tsaro na sa-kai suka yi lokacin da 'yanbindigar suka kai hari kauyen makonni kadan da suka gabata.

A ranar Lahadi, an sace dattawa 39 daga wani kauye a wannan karamar hukumar ta Maradun lokacin da suka kai ziyara sansanin wani shugaban 'yanbindiga domin tattauna yarjejeniyar zaman lafiya da za ta ba al'ummarsu damar noma gonakinsu.

A ranar Talata, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi gargadin cewa yawaitar rashin tsaro da kungiyoyi masu dauke da makamai ke haddasawa na iya "shafar kudaden shiga na gwamnati da na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, tare da kara talauci da rashin wadatar abinci."

Rumbun Labarai
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci a soke shirin gyaran hali na tubabbun 'yan Boko Haram
Jihar Legas ta kama mabarata 396, tana tantance bayanansu domin mayar da su jihohinsu na asali
Nijeriya za ta binciki manyan kamfanonin fasaha kan amfani da labaran ƙasar ba bisa ƙa’ida ba
Gwamnatin Nijeriya ta bai wa 'yan ƙasarta damar ƙarshe ta kwashe su daga Afirka ta Kudu
‘Yansandan Nijeriya sun dakile harin ‘yanbindiga a Sokoto
Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinci
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da fara ayyukan Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru-Ngala
Hukumar INEC ta Nijeriya ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da makwanni biyu
Kotu ta samu mutum biyu da laifin ta'addanci a Nijeriya
Nijeriya ta ƙaddamar da masana'antar sarrafa lithium mafi girma a Yammacin Afirka a jihar Nassarawa
Amurka ta janye akasarin sojojinta da ta aika Nijeriya
Yunwa ta kai mummunan mataki da bai taɓa kai wa ba a shekaru 10 a Arewacin Nijeriya - WFP
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 662, sun ceto 951 da aka sace cikin watanni uku
CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji
Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa 'yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu
Ɗan Nijeriya ya mutu bayan sakinsa daga kurkuku a Côte d'Ivoire
Gwamnatin Nijeriya ta karɓi 'yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga Afirka ta Kudu
Jam'iyyar adawa ta NDC a Nijeriya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu game da rajistarta
Sojojin Nijeriya sun ceto ɗalibai da malaman GDSS Lassa 10 a Jihar Borno
Dakarun Nijeriya sun ce manyan kwamandojin DAESH sun miƙa wuya sakamakon ƙara matsin lambar soji