| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta musanta iƙirarin Amurka da Isra'ila na kashe Jagoran Addini Ali Khamenei
Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi watsi da iƙirarin Netanyahu da Trump, tana mai cewa Shugaban Addini na Iran Khamenei da shugaban ƙasar Pezeshkian suna "cikin aminci da ƙoshin lafiya".
Iran ta musanta iƙirarin Amurka da Isra'ila na kashe Jagoran Addini Ali Khamenei
Khamenei da Pezeshkian suna "cikin aminci da ƙoshin lafiya", in Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran / Reuters

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei ya ce Jagoran Addinin ƙasar Ali Khamenei da shugaban ƙasa Masoud Pezeshkian suna cikin aminci, inda ya yi watsi da iƙirarin Amurka da Isra’ila na kashe su.

Bekayi ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani game da tambayar da gidan talbijin na Amurka ABC News ya yi masa ranar Asabar kan halin da Khamenei da Pezeshkian suke ciki, yana mai cewa suna “cikin ƙoshin lafiya."

Masu AlakaTRT Afrika - Iran ta ƙaddamar da harin makami mai linzami kan Isra'ila da sansanonin Amurka a ƙasashen Larabawa

"Ana gudanar da komai bisa tsarin da muka yi, kuma dakarun ƙasarmu suna yin aikinsu na kare mu daga masu kutse da suka kwashe tsawon rana suna kawo mana hare-hare," in ji shi.

Tun da farko Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi iƙirarin cewa akwai bayanai da dama da suka nuna cewa an kashe Khamenei a hare-haren da ake kaiwa.

Daga baya shi ma Donald Trump ya yi iƙirarin cewa Khamenei ya "mutu."

"Khamenei, ɗaya daga cikin shaiɗanu a tarihi, ya mutu," in ji Trump a saƙon da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social.

"Wannan adalci ne ba ga al'ummar Iran kaɗai ba, har da Amurkawa, da kuma al'ummar ƙasashen duniya waɗanda Khamenei da ‘yan-korensa mashaya jini suka kashe ko suka azabtar,” a cewar Trump.

Trump bai faɗi shaidar da ya dogara da ita wajen bayar da wannan labari ba.

MAJIYA:TRT World and Agencies
Rumbun Labarai
Trump ya ce Amurka za ta iya kai wa Iran sabbin hare-hare
Turkiyya ta kawar da yunkurin jan kasar cikin yake-yaken yankin: Erdogan
WFP ta rage yawan tallafi a Gaza ga mutane 500,000 sakamakon mamayar Isra’ila a yankin
Iran ta ce Netanyahu na ingiza Amurka ga wani yaƙi don kauce wa zaman kurkuku
Tankar mai dauke da ganga fiye da miliyan biyu ta kama da wuta a Mashigar Hormuz
Sojojin Yemen sun kama tawagar masu sarrafa jiragen yaƙi marasa matuƙa na Houthi a Taiz
Mutum 5 sun mutu a hare-haren makamai masu linzami na Houthi a fadar shugaban ƙasar Yemen
An harbo makami mai linzami a sararin samaniyar yankin Madina: Sojojin Ƙawance na Saudiyya
Tarkacen makamai masu linzami na ‘yan Houthi sun jikkata mutum 4, sun lalata gidaje 15 a Saudiyya
Nijeriya ta yi Allah wadai da harin Houthi kan filin jiragen sama na Riyadh a Saudiyya
'Yan Houthi sun kai ƙarin hare-hare a filin jirgin saman Sarki Khalid da ke Riyadh
Mutum 12 sun rasu, 309 sun jikkata bayan harin mayakan Houthi a filin jirgin Riyadh na Saudiyya
Iran na nazarin martanin Amurka kan shirin kwanaki bakwai na sake buɗe Mashigar Hormuz
Ranar 7 ga Oktoba ta fito da raunin Isra’ila: Yaƙin Gaza ya ƙara ta’azzara raunin
Turkiyya da Pakistan sun kaddamar da matakin tsaro na bai-daya don kare Makka daga hare-haren Houthi
Isra'ila na fuskantar barazanar yaƙin basasa, in ji rahoton CIA
Rundunar sojin Yemen ta ce ta kashe 'yan Houthi 260 a hare-haren Taiz da Lahj
Mataimakin matuƙin jirgin FlyDubai ya sari matuƙin jirgi da 'gatari' a harin 'ta'addanci', in ji UAE
Amurka ta tura ƙarin sojoji 9,000 zuwa Gabas ta Tsakiya
Amurka ta tura wa Saudiyya da Qatar ƙarin na’urorin tsaron sama, Patriot don kare wuraren makamashi