Iran ta musanta iƙirarin Amurka da Isra'ila na kashe Jagoran Addini Ali Khamenei

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi watsi da iƙirarin Netanyahu da Trump, tana mai cewa Shugaban Addini na Iran Khamenei da shugaban ƙasar Pezeshkian suna "cikin aminci da ƙoshin lafiya".

By
Khamenei da Pezeshkian suna "cikin aminci da ƙoshin lafiya", in Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran / Reuters

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei ya ce Jagoran Addinin ƙasar Ali Khamenei da shugaban ƙasa Masoud Pezeshkian suna cikin aminci, inda ya yi watsi da iƙirarin Amurka da Isra’ila na kashe su.

Bekayi ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani game da tambayar da gidan talbijin na Amurka ABC News ya yi masa ranar Asabar kan halin da Khamenei da Pezeshkian suke ciki, yana mai cewa suna “cikin ƙoshin lafiya."

"Ana gudanar da komai bisa tsarin da muka yi, kuma dakarun ƙasarmu suna yin aikinsu na kare mu daga masu kutse da suka kwashe tsawon rana suna kawo mana hare-hare," in ji shi.

Tun da farko Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi iƙirarin cewa akwai bayanai da dama da suka nuna cewa an kashe Khamenei a hare-haren da ake kaiwa.

Daga baya shi ma Donald Trump ya yi iƙirarin cewa Khamenei ya "mutu."

"Khamenei, ɗaya daga cikin shaiɗanu a tarihi, ya mutu," in ji Trump a saƙon da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social.

"Wannan adalci ne ba ga al'ummar Iran kaɗai ba, har da Amurkawa, da kuma al'ummar ƙasashen duniya waɗanda Khamenei da ‘yan-korensa mashaya jini suka kashe ko suka azabtar,” a cewar Trump.

Trump bai faɗi shaidar da ya dogara da ita wajen bayar da wannan labari ba.