| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Jihohi 12 da Tinubu zai je yaƙin neman zaɓen Nijeriya na 2027
A wajen liyafar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Laraba, Tinubu ya ce ba dukkan gangamin yaƙin neman zaɓen zai halarta ba, domin kada hakan ya ɗauke hankalinsa daga hidimar da yake yi wa ƙasar.
Jihohi 12 da Tinubu zai je yaƙin neman zaɓen Nijeriya na 2027
Tinubu zai fara yaƙin neman zaɓensa ne a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Nijeriya

Shugaba Bola Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki ne a jihohi 12 gabanin zaɓukan 2027.

Jadawalin yaƙin neman zaɓen da jam’iyyar APC ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa ana tsamminin Tinubu ya ƙaddamar da kamfe ɗin sake zaɓensa ne a jihar Kaduna ranar 24 ga watan Oktoba kafin ya halarci gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohi 11.

Bayan gangamin yaƙin neman zaɓen na Kaduna, shugaban zai halarci kamfe a jihar Ribas da ranar 7 ga watan Nuwamba da Filato 14 ga watan Nuwamba da Oyo a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Ana kuma sa rai zai halarci yaƙin neman zaɓe a jihohin Borno da Enugu da Bauchi a ranakun 25 da 28 da kuma 29 ga watan Nuwamba.

Sai dai kuma Tinubu ba zai halarci kamfe ba a jihohi 13 a cikin watan Nuwamba, kamar yadda jadawalin ya tsara.

Jihohin su ne Cross River (2 ba watan Nuwamba) da Gombe (3 ga watan Nuwamba) da Nasarawa (4 ga watan Nuwamba) da Ekiti (5 ga watan Nuwamba) da Ebonyi (9 ga watan Nuwamba) da Jigawa (10 ga watan Nuwamba) da Ondo (11 ga watan Nuwamba ) da Edo (12 ga watan Nuwamba ) da Yobe (16 ga watan Nuwamba) da Kebbi (17 ga watan Nuwamba) da Akwa Ibom ( 18 ga watan Nuwamba ) da Anambra (19 ga watan Nuwamba) da Benue (30 ga watan Nuwamba).

Ana sa ran Tinubu zai ci gaba da kamfe ɗinsa a watan Disamba da gangamin da aka shirya yi a jihar Sokoto ranar 5 ga watan Disamba da jihar Delta a ranar 12 ga watan Disamba da kuma jihar Kano a ranar 17 ga watan Disamba.

Zai ƙarƙare fita yaƙin neman zaɓen ne a jihar Adamawa ranar 4 ga watan Janairu da kuma jihar Legas ranar 9 ga watan Janairu, yayin da shuwagabannin jam’iyyar za su wakilce shi a gangamin yaƙin neman zaɓe a sauran jihohi 12 a watan Disamba.

Jumulla dai ana sa rai Tinubu zai halarci yaƙin neman zaɓe ne a 12 daga cikin jihohin Nijeriya 36 da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Huɗu daga cikin jihohin da ake sa ran Tinubu zai ziyarta — Kano da Oyo da Bauchi da Adamawa — suna da jigajigan ‘yan siyasar jam’iyyun hamayya da ke alaƙa da takarar shugaban ƙasa ta 2027.

Tsohon gwmanan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ɗantakararn mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC kuma ɗan jihar Kano ne.

Shi kuwa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya kuma ɗantakarar shugaban ƙasa a jami’yyar ADC, Atiku Abubakar, ɗan jihar Adamawa ne.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, shi ne ɗantakarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APM, wadda ita ce jam’iyya mai mulki a jihar Bauchi.

A wajen liyafar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Laraba, Tinubu ya ce ba dukkan gangamin yaƙin neman zaɓen zai halarta ba, domin kada gangamin ya ɗauke hankalinsa daga hidimar da yake yi wa ƙasar.

Sai dai kuma ya ce zai ware lokaci wajen magana kai-tsaye da ‘yan Nijeriya yayin da shuwagabannin jam’iyyarsa ke yawo a faɗin jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar wajen yaƙin neman sake zaɓarsa.

A ranar Talata ne dai APC ta ce ta faɗaɗa jerin sunayen ‘yan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar inda ta ƙara sunayen ministan Abuja Nyesom Wike da gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke da gwamnan jihar Anambara Chukwuma Soludo a cikin wasu manyan ƙusoshi da ta ƙara.

Rumbun Labarai
'Yansanda sun kama mutum 103 da ƙwayoyi da makamai a jihar Borno ta Nijeriya
Rundunar ’yansandan Nijeriya ta gargaɗi ’yan siyasa kan lalata kayan kamfen gabanin zaɓen 2027
EFCC ta bankaɗo haramtacciyar matatar mai da ake zargin ’yan China suna gudanarwa a Jihar Ogun
'Yansanda sun bankaɗo wurin buga jabun daloli, sun kama mutum ɗaya a Ondo
Asusun gwamnatin Tarayyar Nijeriya na N10b ba na cutar Ebola kaɗai ba ne, in ji shugaban NCDC
Gwamnatin Nijeriya ta kama wasu da ake zargi da aikin rajistar lambar NIN ba bisa ƙa'ida ba
Sojojin Nijeriya sun kashe manyan Shugabannin Daesh a Borno
’Yanbindiga sun sace kimanin yara 12 a Jihar Neja
Gwaji ya tabbatar mutum biyu da ake zargin suna ɗauke da Ebola a Adamawa ba su da cutar - NCDC
’Yansanda sun dakile harin ‘yanta'adda a Zamfara, sun gano gawarwaki fiye da 30
An gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Arewa maso Gabashin Nijeriya
INEC ta wallafa sunan Pantami a shafinta na ’yantakarar gwamna amma babu Gwarzo na Kano
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da shirin tallafin kuɗi na N50,000 ga ’yan ƙasar da ke cikin talauci
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda Daesh 48, sun ƙwato makamai a jihohin Borno da Yobe
Wani sufeton ‘yansanda da fararen-hula 11 sun rasa rayukansu a wasu hare-haren ta’addanci a Kebbi
Tinubu ya kare matakin karɓo bashi daga waje, ya ce Nijeriya na buƙatar haɓaka tattalin arziki
NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu da haramta amfani da su na Naira Biliyan 8 a Jihar Nasarawa
Dakarun Nijeriya sun ce sun kashe ‘yanta’adda 42 a arewa maso gabashin ƙasar
Nijeriya ta amince da biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya naira 70,000 kudin sufuri duk wata
Mutane daga kasashe 120 na duniya ciki har da na Afirka 54 sun sayin hannayen jari a Matatar Dangote