Dalilin da ya sa har yanzu kuturta ke cikin cututtukan da ke addaba da barazana ga ɗan'adam

Hukumar (WHO), wacce ke bikin Ranar Kuturta ta Duniya a duk Lahadin ƙarshe watan Janairu don daƙile tsangwama da kuma nuna ci gaban kimiyya kan cutar, ta ce duk da ana iya warke wa daga cutar, tsoro da wariya sune manyan ƙalubalen da ake fuskanta

By
Kuturta cuta ce da ake samu daga ƙwayoyin halitta da ke shafar fata da jijiyoyi. / Reuters

Gano cutar kuturta da Tinasoa Rakotoarimanana ta yi shekaru biyu da suka gabata ba ta tsaya ga iya damuwar da ta tsinci kanta a ciki ba bayan sanin cewa tana da cutar, sai ta yadda za ta shawo kan ƙalubalen da ke gabanta.

Matashiyar, wacce a lokacin take da shekaru 24, ta ɗauka yadda fuskantar ke sauya launi zuwa ja bai da wani lahani. Sai da ta soma jin yatsunta ba sa aiki, shi ne Tinasoa ta yanke shawarar zuwa ganin likita.

Ziyarar da ta kai wani asibiti a garin Miarinarivo da ke tsakiyar Madagascar ta jefa ta cikin tashin hankali. Gwaje-gwaje sun tabbatar da cewa tana da cutar kuturta, wata annoba da ta yi tunanin tana nesa da ita a wata duniya.

"Na yi kuka. Na ji kamar rayuwata ta tsaya cak," kamar yanda Tinasoa ta shaida wa TRT Afrika game da wannan mummunan lokacin da ta ji sakamakon gwajin da aka yi mata a asibiti. "Nan da nan na ji tsoron cewa babu wanda zai so ya sake kasancewa tare da ni."

Kamar yadda take jin tsoro, yayin da labarin ya bazu a cikin al’ummar da ta fito, Tinasoa ta ga yadda aka ƙyamaceta tare da nuna mata wariya kan cutar. Abokai da ƙawaye suka daina gayyata da kuma zuwa wajenta.

"Wasu mutane a ƙauyenmu sun yi zargin cewa muna da cutar kuturta a zuri’armu. Wasu kuma sun kira hakan da asiri. Gaskiyar maganar ita ce, babu wanda ya taɓa kamuwa da cutar a cikin zuri’armu," in ji ta.

A wani gari kuma, Solo Andrianirina mai shekaru 32 ya fuskanci makamancin irin wannan matsala lokacin da ya fahimci cewa ya kamu da cutar kuturta.

"Na ji tsoro sosai. A gare ni, kuturta cuta ce daga wani zamani da ba ni da wata alaƙa da ita. A yanzu da aka shaida min cewa ta mamaye jikina, nan da nan na yi tunanin wariya da kuma ƙyama da zan fuskanta," in ji shi a hirarsa da TRT Afrika.

Daɗaɗɗiyar cuta, maganin zamani

Kuturta wata cuta ce da ake samu daga ƙwayoyin cuta da ke shafar fata da jijiyoyi. Idan ba a yi magani ba, tana lalata jijiyoyi, da nakasa mutum da sauya halitta.

Duk da cewa a tarihin ɗan’adam kuturta na ɗaya daga cikin cututtukan da aka daɗe da sani, a yanzu cutar ba ta zama ƙalubalen lafiyar jama'a a duniya ba saboda ci gaban da aka samu na magani.

A mafi yawan lokuta, ana iya warkar da cutar gaba ɗaya ta hanyar tsarin magunguna masu yawa, wanda ake bayarwa kyauta a yawancin ƙasashen duniya.

Duk da haka ingancin maganin zamani bai kawar da tsoro da tsangwama daga al’umma game da batun da ke da alaƙa da kuturta ba.

Har yanzu tsangwama tana sa masu larurar keɓe kansu, tana sa su rasa aiki da ilimi, kuma wani lokacin tana sa iyalansu su ƙi su.

"‘Yan’uwana sun ba ni goyon baya sosai amma wasu abokai sun guje ni," in ji Solo.

Ya ƙara da cewa "wasu har yanzu suna ganin cutar tana yaɗuwa kuma za su kamu da kuturta ta hanyar taɓa ni kawai. Ina jin zafin hakan, kodayake na fahimci cewa galibi saboda rashin wayar da kai ne."

Yanayin da Tinasoa ta tsinci kanta ya fi muni a kan na Solo. "Mahaifiyata ta tsaya min amma sauran mutane sun guje ni. An gaya min kada in zo taro. Na ji takaici. Amma a yanzu na san cewa cuta ce da za a iya warkewa, kuma ina son wasu su fahimci hakan ma,’’ in ji ta.

Shiru da nauyi na rayuwa

A ƙasashen da har yanzu kuturta ke da gindin zama, nauyi na rayuwa kan cutar yana hana iya gano cutar da wuri, tare da barin alamominta su tsananta kuma ya ci gaba da yaɗuwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), wacce ke bikin Ranar Kuturta ta Duniya kowace Lahadin ƙarshen wata Janairu don daƙile tsangwama da kuma bayyana ci gaban kimiyya kan cutar, ta bayyana cewa duk da ana iya warkewa daga cutar, tsoro da nuna wariya sun kasance manyan kalubale da ake fuskanta.

Jigon ranar ta wannan shekarar ita ce - "Ana iya warkewa daga Kuturta, babban ƙalubalen shi ne ƙyama." - Yana nuna dalilan da suka sa wayar da kai kan kuturta ke da matukar muhimmanci ga lafiyar jama'a duk da ci gaba da aka samu shekaru da dama.

Bisa bayanan WHO, an gano ƙarin masu cutar har 21,043 a Afirka a shekarar 2023, wanda ke wakiltar kashi 11.5% na yawan adadin a duniya.

Yawancin ƙasashe sun cim ma nasarar kawar da kuturta a matsayin matsalar lafiyar jama'a a hukumance, inda ma'aunin ya nuna cewa cutar ta fi ƙamari ne a tsakanin mutum ɗaya cikin mutum 10,000.

A Afirka, har yanzu akwai wuraren da ake kamuwa da cutar, musamman a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, da Habasha, da Madagascar, da Mozambique, da Nijeriya da kuma Tanzania.

Kodayake yawan kamuwa da kuma gano cutar na raguwa, sai dai ana ci gaba da samun rahotannin yaduwar cutar, da ganowarta a makare da kuma nakasa da ke da alaƙa da ita a faɗin waɗannan ƙasashe.

A shekarar 2023, fiye da masu cutar 3,000 a nahiyar musamman masu nakasa a mataki na 2, sun nuna jinkirin gano cutar.

Rashin fahimta na ƙara haifar da son zuciya

Batun cewa ba haka kawai ake samun cutar ba yana ƙara sanya a kyamace duk wanda ke tattare da ita.

Da yawa daga cikin masu fama da cutar sun gwammace su ɓoye alamominta fiye da su fuskanci wariya da rashin fahimta game da cutar kuturta wadda ba ta yaduwa cikin sauri kamar yadda ake daukarta.

Kuturta tana yaɗuwa ta hanyar ‘yan ɗigo-ɗigon ƙwayoyin cuta da ake samu ta iska sa’ilin da masu ɗauke da cutar suka yi tari ko atishawa.

Shan hannu ta hanyar gaisawa da runguma ko cin abinci tare da zama kusa da mai dauke da cutar duk ba sa haifar da kuturta. Fiye da kashi 95% na mutane da rigakafin cutar na halitta.

WHO ta gudanar da gangami da dama da ke nuna cewa kuturta ba ta yaɗuwa kamar tarin fuka, COVID-19 ko cutar ƙyanda.

Da zarar an fara magani, cikin sauri marasa lafiya suke daina zama cikin haɗarin yaɗa cutar. Sai dai duk da haka, tsoron ƙyama da wariya suna hana mutane da yawa neman taimako, wanda hakan ke janyo ƙalubale da ci gaba da yaɗa cutar.

Da Tinasoa da Soklo duk sun warke, a yanzu suna son wasu ma su san abubuwan da ba sani ba lokacin da cutar kuturta ta katse musu rayuwarsu.