Zarge-zargen da hukumar ICPC ke yi wa Nasir El-Rufai

A ranar Talata ne ICPC ke gurfanar da Nasiru El-Rufai a gaban kotu tun lokacin da ta kama shi a watan Fabrairu bayan hukumar EFCC ta sake shi.

By
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya sha zargin gwamnatin Nijeriya da yi masa bi-ts-da-ƙullin siyasa don ya fita daga Jam'iyyar APC / Reuters

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (ICPC) ta ce za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ranar Talata.

Hukumar ta bayyana cewa ta gabatar da takardar tuhuma da ke ƙunshe da zarge -zarge ciki har da mayar da kadarar gwamnati tashi tare da halasta kuɗin haram a gaban kotun ranar 18 ga watan Maris .

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, mai magana da yawun bakin ICPC, John Okor Odey, ya ce za a gurfanar da El-Rufai ne tare da wani mai suna Joel Adoga.

Ya kuma bayyana cewa an shigar da wata ƙarar ta daban kan tsohon gwamnan a wata babbar kotun jihar Kaduna, wadda ke da alaƙa da ci da amfani da muƙami wajen halatsa haram da damfara da kuma niyyar aikata damfara domin samun abin da bai kamata ba.

Hukumar ta ce daga baya za a sanar da ranar da za a gurfanar da shi a gaban kotun jihar.

“Kazalika an shigar da wata takardar tuhumar mai lamba KDH/KAD/ICPC/01/26, kan Malam Nasir El-Rufa’i da kuma wani mai suna Amadu Sule (LEDA), a gaban wata babbar kotun jihar Kaduna,” in ji sanarwar.

“Tuhume-tuhumen da aka shigar babbar kotun jihar sun haɗa da amfani da muƙami domin aikata ba daidai ba da damfara da niyyar aikata damfara domin samin abin da bai dace ba da sauransu.

Takardun tuhume-tuhumen biyu dai ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2026 ne hukumar ICPC ta shigar da su .

“Za a sanar da ranar gurfanarwa a gaban babban kotun jihar a lokacin da ya dace da kotun za ta saka.

“Hukumar ICPC na son ta sanar da mutane cewa an riga an bai wa Mallam Nasir El-Rufa’i takardun tuhumar. Hukumar ICPC ta sake jaddada jajircewarta kan bin matakan da suka dace da kuma biyayya ga doka a ko wane lokaci,” in ji sanarwar.

Tun bayan hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin azriƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ta sake shi dai a watan Fabrariru , tsohon gwmanan na jihar Kaduna ya kasance a hannun hukumar ICPC ne.

Ranar 5 ga watan Maris, wata kotun majistire ta ba da damar a tsawaita riƙe shi na tsawon kwanaki 14, lamarin da ya tsawaita riƙe shi fiye da umarnin kotu na farko.

Lamarin dai ya janyo matsi kan hukumar, inda mutane da yawa musamman daga jam’iyyar adawa ke kira ga hukumomi su gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma su sake shi.