Hamas ta ce harin Isra'ila ya kashe babban mai magana da yawunta a lokutan yaƙi, Abu Ubaida
Abu Ubaida da kulluma fuskarsa ke rufe kuma ba kasafai ake ganinsa a bainar jama'a ba, shi ne wanda aka fi jin muryarsa a duk tsawon lokacin da aka shafe ana yaƙi, inda yake yawan aika saƙonnin da ke isa ga al'ummar duniya.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta tabbatar da mutuwar Abu Ubaida, mai magana da yawunta da ak fi sanin muryarsa sosai a lokacin yaƙi, tare da wasu manyan kwamandoji na soja da suka mutu a yayin yakin Isra'ila na tsawon shekaru biyu a Gaza.
A cikin wata sanarwa da aka saki a ranar Litinin, reshen soji na Hamas Qassam ya ce Abu Ubaida — wanda sunansa na gaskiya shi ne Hudhayfah Abdullah al-Kahlout — ya mutu a cikin rikicin.
Abu Ubaida da kulluma fuskarsa ke rufe kuma ba kasafai ake ganinsa a bainar jama'a ba, shi ne wanda aka fi jin muryarsa a duk tsawon lokacin da aka shafe ana yaƙi, inda yake yawan aika saƙonnin da ke isa ga al'ummar duniya.
Kungiyar ta kuma tabbatar da mutuwar babban shugaban ma'aikata, Mohammed Sinwar, wanda ya jagoranci Rundunar Qassam a abin da Hamas ta bayyana a matsayin "lokaci mai matuƙar wahala" bayan da ya gaji tsohon kwamanda Mohammed Deif wanda ya fi daɗewa a matsayin.
Sinwar ɗan'uwan Yahya Sinwar ne, shugaban siyasa na Hamas a Gaza.
An tabbatar da mutuwar wasu manyan kwamandojin
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Mohammed Shabana, kwamandan rundunar Rafah, wanda Hamas ta ce ya mutu tare da Yahya Sinwar.
Kungiyar ta kuma sanar da mutuwar Hakam al-Issa, babban jigo mai hannu a horo, ilimin soja da tsara dabaru, da kuma Raed Saad, wanda aka bayyana a matsayin shugaban sashen ƙera makamai na Hamas kuma tsohon shugaban ayyuka.
Hamas ta bayyana waɗannan asarori a matsayin shaida ta babbar asarar da ta tafka a shugabancinta a lokacin yaki, kuma ta ce mutuwar ba za ta raunana juriyarsu ba.