| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Mali tana binciken sojoji da ’yan siyasa da ke da alaƙa da hare-haren ta’addanci
Hukumomi sun bayyana cewa ana kama mutane yayin da bincike kan tsararrun hare-haren yake ƙara faɗaɗa.
Mali tana binciken sojoji da ’yan siyasa da ke da alaƙa da hare-haren ta’addanci
Mali ta gudanar da jana'izar ban girma ga ministan tsaro da aka kashe / Reuters

Rundunar sojin Mali ta bayyana a ranar Juma’a cewa ta ƙaddamar da bincike kan hare-haren ta’addanci na ranar 25 ga watan Afrilu da aka kai a sassa daban-daban na ƙasar, inda sakamakon farko na binciken yake nuna zargin hannun sojoji da ’yan siyasa wajen tsarawa tare da aiwatar da hare-haren.

Sojojin sun bayyana cewa an kai jerin hare-haren a cibiyoyin sojojin Mali da dama, ciki har da wurare a babban birnin ƙasar, Bamako, da Kati, da kuma gidan Ministan Tsaro da Al’amuran Tsoffin Sojoji, Sadio Camara.

“Binciken da aka gudanar ya nuna ƙwararan shaidu dangane da haɗin baki na wasu jami’an soja, da korarrun sojoji, ko kuma waɗanda ke jiran kora, wajen aiwatar da hare-haren,” in ji mai gabatar da ƙara na soja.

Bayanin ya ci gaba da ambato “shigar wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da Dokta Oumar Mariko”.

Yadda aka gudanar da kamen mutane

Mai gabatar da ƙarar ya bayyana cewa an yi kamen farko-farko cikin nasara, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargi ruwa-a-jallo.

Mali ta fuskanci ƙalubalen tsaro da yaƙi-ci-yaƙi cinyewa tun shekarar 2012, waɗanda ke haifar da hare-hare a kai-a-kai da ake kai wa wuraren sojoji da na farar hula.

Hare-haren na ranar 25 ga watan Afrilu sun kasance babban koma baya ga tsaro saboda girmansu da kuma yadda suka shafi manyan wurare, ciki har da gidan ministan tsaro.