Wasu jiragen ruwa suna sauya hanya daga Mashigar Hormuz zuwa ta Oman
Kimanin jiragen ruwa 15 ne suka wuce ta hanyar cikin sa’o’i 24 kawo misalin ƙarfe 0900 agogon GMT, inda kimanin 10 suka fice daga mashigin , in ji bayanai da ke akwai.
Wasu jiragen ruwa sun ja da baya a mashigin ruwan Oman duk da kai-komon da ake yi ta Mashigar Ruwan Hormuz, in ji bayanai na bibiyar jiragen ruwa.
Duk da cewa tafiye-tafiye na ci gaba a hanyar ruwan mai muhimmanci, wasu jiragen ruwa da suka shiga Mashigar Ruwan Oman— da ke haɗa mashigin ruwan da tekun Larabawa —sun juya sun koma ta mashigin ruwan.
Kimanin jiragen ruwa 15 ne suka wuce ta hanyar cikin sa’o’i 24 da misalin ƙarfe 0900 agogon GMT, inda kimanin 10 suka fice daga mashigin, in ji bayanai da ke akwai.
Tsakanin jiragen ruwan da ke wucewa ta hanyar akwai wasu tankoki da kuma jiragen ruwa na dako da ke tafiya tsakanin nahiyar Asia da Gabas ta Tsakiya.
Wasu na kan hanayarsu daga ƙasashe irin su India da China da Malaysia da Brazil da Oman, inda suka nufi wurare ciki har da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Iran da Iraƙi.
Sai dai kuma, aƙalla jirgin ruwa ɗaya da ya shiga mashigin ruwan Oman daga baya ya sauya hanya kuma ya koma ta mashigin biyo bayan ƙawanyan sojin ruwa na Amurka.
Sannan kuma an samu bayanin tafiyar ƙarin jiragen ruwa na dakon abubuwa da kwantenoni tsakanin tashoshin jiragen ruwa, ciki har da hanyoyin da suka haɗa Iran da Libya da sauran ƙasashen Larabawa na gaɓar teku.
Dakarun sojin ruwan Amurka sun tabbatar da ƙawanyar a kan wata hanya daga sashin tekun Gwadar kusa da kan iyakar Iran da Pakistan zuwa Ras al Hadd na Oman, inda kaikomo na jiragen ruwa mai yawa ya ci gaba.
Hedikwatar ba da umarni ta tsakiya ta sojin Amurka ta ce fiye da jami’an Amurka 10,000 da goyon bayan jiragen ruwa na yaƙi da jiragen sama na yaƙi, suna tabbatar da aikin na neman taƙaita shiga da ficen jiragen ruwa daga tashoshin jiragen ruwan Iran.
Sojin ta ce cikin sa’o’i 24 , babu wani jirgin ruwa da ya samu ya wuce ta ƙawanyar, yayin da wasu jiragen ruwa na ‘yan kasuwa suka bi umarnin dakarun Amurka na komawa tashoshin jiragen ruwan Iran.