"Ina ma a ce abubuwan da suka faru a siyasar Kano mafarki ne": Kwankwaso
Jagoran Jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano a Nijeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana irin yadda ya ji da ma halin da ya tsinci kansa a ciki bayan da gwamna ɗay na jam’iyyarsu Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Jagoran Jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano a Nijeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana irin yadda ya ji da ma halin da ya tsinci kansa a ciki bayan da gwamna ɗay na jam’iyyarsu Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
A wata hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa, kuma hirarsa ta farko tun fara dambarwar ficewar Abba daga NNPP wadda ya ci zabe a ƙrƙashinta, Kwankwaso ya bayyana cewa abubuwan da suka faru sun kasance na rashin jin dadi da takaici.
Tsohon gwamnan na Kano ya tunatar da cewa da yawa daga jama’a da farko sun fara tunanin wani ƙulli ne shi da gwamna Abba suka shirya a fagen siyasar Kano da ma Nijeriya, yana mai cewa “Da yawa mutane ba su yarda da gaske ba ne. Ni ma kaina sau da yawa ba na yarda cewa abubuwan da suke faruwa haka suke.”
Cikin alhini da bayyana rashin jin dadi, Kwankwaso ya shaida cewa “Wani lokacin da yawa sai na farka daga bacci, sai na yi tunanin ina ma a ce abin duka mafarki ne….amma jiya na samu labarin ya (Gwamna Abba) fita daga jam’iyarmu ta NNPP ya koma APC.”
“An dauki hakkokinmu da guminmu an kai wa makiyanmu”
Da aka tambayi Kwankwaso ko zai iya bayyana babban abin da ya fi ba shi haushi kan komawar Gwamna Abba jam’iyyar APC, tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya Kwankwaso ya bayyana cewa babban abin takaici shi ne baya ga barin su da Abba ya yi, sai ga shi ya koma Gandujiyya (gidan siyasar tsohon gwamnan Kano Ganduje).
Ya ce “Ni kaina idan na kwanta sai na waiwaya na ce me ya faru, waye ya yi laifi? Ni ne na yi laifi? Jam’iyya ce ta yi laifi? ‘Yan jam’iya ne suka yi laifi? Wadannan abubuwa na kasa samun amsa.”
Kwankwaso ya kuma ce dukkan abubuwan da gwamna Abba ya fada masa da wadanda ya turo a fada masa, ba su wuce wadanda za a hadu a gyara ba saboda ana tafiya tare.
“A wannan aikin dai mu muka yi aiki, muna da hakki, ba za ka ce a dauka a kai wa ‘yan Gandujiyya da muka sha yaki da su dare da rana ba….shi ne babban rashin adalci, a ce a dauki aikin da ka yi a kai wa makiyanka,” ya fada cikin ban ta’ajibi.”
“Wannan matsala ba za ta lalata zumuncinmu ba”
Kasancewar Gwamna Abba ya zauna da Kwankwaso na shekaru 40, kuma gwamnan suruki ne a wajen sa, an tambayi Kwankwason ko wannan sauyin sheka da Gwamna Abba ya yi zai lalata zumuncinsu, amma sai ya ce ba ya tunanin hakan zai bata zumunci.
Kwankwaso ya kuma fayyace batun ayyana ranar 23 ga kowanne Janairu a matsayin ranar butulci ta duniya, inda ya ce ba shi ya ce a yi hakan ba, amma ya bayyana goyon bayansa ga kiran a yi hakan.
Ya ce ya bayar da goyon bayan ne saboda ‘yan baya, domin ya kamata masu zuwa a nan gaba su san me ya faru da yadda abubuwa suka kasance.
Ya kara da cewa wannan abu marar dadi ya bata wa mutane rai, musamman ‘yan Kwankwasiyya, kuma suna ta kokarin su kwantar da hankulan magoya baya.
“Babu jam’iyyar da ba ta da rikici a cikinta”
Kwankwaso ya kuma tabo batun rikicin jam’iyyar NNPP, wanda ake cewa na daga cikin dalilan da suka sanya gwamna Abba sanya kafa ya bar ta.
Ya ce “Jam’iyyarmu kalau take, ba mu da wani rikici, saboda akwai shugabanci nigari.”
Ya ci gaba da cewa siyasa ake yi, a yanzu babu wata jam’iyya da ta fi NNPP zaman lafiya, kuma su ma ‘yan APC da zarar zun gudanar da babban taronsu, a nan za a gano suna cikin matsala.
Madugun Kwankwasiyyar ya ci gaba da cewa a yanzu haka jama’ar Kano na ci gaba da nuna kauna ga tsarin Kwankwasiyya, kuma duk wanda zai zo da wani zance to za su ba shi amsar da ta dace.
“Duk wanda ya bi Abba APC ba dan Kwankwasiyya ba ne, kuma Ganduje ne zai kayar da Abba a 2027”
Da aka tambayi Kwankwaso kan wadanda suka bi gwamnan Kano zuwa APC, amma suka ci gaba da saka jar hula sai ya ce, a yanzu a Kano akwai haske da duhu, duk wanda ya tafi duhu ya bar haske to kansa ya yi wa, tsarin Kwankwasiya daban, akidarta ma daban take da sauran.
Ya ce idan za ka yi Kwankwasiyya ka tsaya a inda take ka yi ta, ba sai ka koma wani waje ba.
“Duk wanda ya tafi to ka zama dan Gandujiyya, ka narke, haka za mu gan ka, haka jama’a za su gan ka, kamar yadda muke ganin Ganduje, ko ka saka jar hula, ko ba ka saka ba,” in ji Kwankwaso.
Ya kuma ce an nuna masa a takarda yadda Ganduje ya daga hannun Abba, a saboda haka wannan ne ma zai sanya shi faduwa zabe, saboda da a ce Ganduje na da hannun dagawa, da ya daga a 2019, da ya daga a 2023.
A karshen Kwankwaso ya ce suna nan suna aikin don ganin an samu damar saita Nijeriya a samu mafita a kasar.