Yayin da manyan zaɓukan shekarar 2027 ke ƙaratowa, jam’iyyun siyasa sun sami sauƙi bayan wata kotun tarayyar Nijeriya a Abuja ta soke jadawalin da hukumar zaɓe INEC ta fitar na gudanar da zaɓukan fid da gwani da tsayar da ‘yantakara.
A hukuncin da ya yanke, alƙalin kotun, Mai shari’a Mohammed Umar, ya soke wa’adin ranar 10 ga watan Mayu da INEC ta gindaya, wa’adin da ke buƙatar dukkan jam’iyyu su miƙa rijistar dukkan mambobinsu a matsayin sharaɗi na samun damar shiga zaɓuka.
Jaridar Vanguard ta ambato wani tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa, Gbenga Hashim yana cewa hukuncin kotun da ya soke wasu ɓangarori daga cikin jadawalin hukumar Zaɓe INEC na zaɓen 2027 ya gaskata matsayarsa daɗaɗɗiya cewa, hukumar zaɓen ta zarce wuce gona da iri a ƙarƙashin dokar zaɓe ta shekarar 2026.
Mai shari’a Umar ya ce wa’adin da hukumar ta sanya wa jam’iyyun siyasa na gudanar da zaɓukan fid da gwani kuma su miƙa, da janye ko kuma maye gurbin sunaye da bayanan ‘yantakara domin manyan zaɓukan “bai dace da tanade-tanaden dokar zaɓe ta shekarar 2026 ba.”
Hukuncin ya biyo bayan wata ƙara da jam’iyyar YP ta shigar, inda ta nemi a tilasta wa INEC ta yi biyayya ga wa’adin kwanaki 120 na miƙa rijistar ‘yanjam’iyya da bayanan ‘yan takara gabannin zaɓe, bisa dokar zaɓen 2026.
Mai shigar da ƙarar ya nemi kotun ta ayyana cewa idan aka yi la’akari da tanade-tanaden sashi na 29, 82 da sashi na 84(1) na dokar zaɓen shekarar 2026, ikon INEC na karɓar sanarwar zaɓukan fid da gwani da bayanan ‘yan takara da kuma nauyin da ya rataya a kanta na halarta da sa ido kan zaɓukan fid da gwani bai kai ga saka rana ko kuma jadawali na zaɓukan fid da gwani cikin jam’iyyu domin tsayar da ‘yan takara a zaɓukan shekarar 2027 ba.
Maishari’a Umar ya kuma yanke hukuncin cewa a tanade-tanaden sashi na 32 na dokar zaɓe ta shekarar 2026, INEC ba ta da ikon wallafa sunayen ‘yantakara na ƙarshe na zaɓukan 2027 kafin aƙalla kwanaki 60 gabannin zaɓen kamar yadda doka ta tanada.

















