| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Wani sanatan Amurka ya fada wa Majalisar Dattawa cewa ƙasar ta yi asarar jirage 39 a yakin Iran
Dan majalisar dokokin Amurka Ed Case a ranar Talata ya bayyana cewa Amurka ta yi asarar jiragen sama 39 tun bayan fara yakin Iran a ranar 28 ga Fabrairu, yana mai rawaito wani rahoton tsaro.
Wani sanatan Amurka ya fada wa Majalisar Dattawa cewa ƙasar ta yi asarar jirage 39 a yakin Iran
Wani sanatan Amurka ya fada wa Majalisar Dattawa cewa ƙasar ta yi asarar jirage 39 a yakin Iran / Reuters


Dan majalisar dokokin Amurka Ed Case ya ce Washington ta yi asarar jiragen sama 39 a yayin yaki da Iran, yana mai rawaito wani rahoto na tsaro wanda Pentagon ba ta tabtabbatar da shi a hukumance ba.

Dan majalisar dokokin Amurka Ed Case a ranar Talata ya bayyana cewa Amurka ta yi asarar jiragen sama 39 tun bayan fara yakin Iran a ranar 28 ga Fabrairu, yana mai rawaito wani rahoton tsaro.

Case ya fadi haka a wajen zaman majalisar dattawa na musamman yayin tambayar Babban Jami’in Kudi Jay Hurst game da asarar da aka tafka a lokacin yakin.

“Mun yi asarar kimanin jiragen yaki 39, kamar yadda wani rahoton yakin ya bayyana, kuma tsohon rahoto ne na kusan wata guda, ya fada yana tambayar Hurst ko Pentagon ta lissafa asarar da aka yi.”

Hurst ya bayar da amsa da cewa “An yi asara, amma zan dawo gare ka a rubuce kan ko nawa ne, saboda kamar yadda za ka iya tunawa, yana da wahala a iya lissafa nawa za a kashe wajen gyara jirgin sama.”

“Dole sai mun yi nazari sosai kan jirgin kafin mu lissafa nawa za a kashe don gyara shi.” In ji shi.

Rahoton da Case ya rawaito, wanda kafar labaran tsaro ta Amurka ta The War Zone ta buga, ya ce Amurka ta tashi jiragen sama sau 13,000 yayin yaki da Iran.

Rahoton ya kuma ce an lalata jiragen sama na yaki 39, kuma wasu 10 sun raunata.
Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa an harbo jirgin F-35A a sararin samaniyar Iran, kuma an lalata jirgi samfurin Boeing E-3.

Ba a tabbatar da sahihancin rahoton ba, kuma Pentagon ba ta ce komai a kai ba.
A ranar 28 ga Fabrairu ne Amurka sa Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran, wanda ya janyo martani daga Tehran a kan kadarorin Amurka da Isra’ila da ke kasashen Gulf da ma rufe mashigar teku ta Hormuz.

A ranar 8 ga Afrilu an amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar shiga tsakanin Pakistan, amma tattaunawa a Islamabad ta rushe tare da gaza samar da dauwamammiyar tsagaita wuta.