Arzikin attajiran Afirka na ƙaruwa sosai. Ya ƙaru da aƙalla kashi 56 cikin 100 a cikin shekaru biyar da suka gabata kawai.
A wani abin da ya sha bamban da lamarinsu, talakawa suna daɗa talaucewa. Wani rahoton da gamayyar ƙungiyoyi masu zaman kansu ta Oxfam International ta yi a shekarar 2025, ‘yan Afirka huɗu da suka fi arziki sun fi jummular mutum miliyan 750 a nahiyar arziki. Wanna shi ne rabin yawan mutanen nahiyar.
Afirka ba ta da attajirai da aka sani da sama da dala biliyan ɗaya a bayyane zuwa shekarar 2000. A halin yanzu akwai aƙalla 23 masu irin wannan arzikin.
Mujallar Forbes ta ce kimar kuɗin mutanen ya kai dala biliyan $126.7 zuwa watan Mayun shekarar 2026. Wannan shi ne ƙarin kashi 21 cikin 100 daga shekarar da ta gabata.
Daga Aliko Dangote da Abdul Samad Rabiu na Nijeriya da ‘yan Afirka ta Kudu Johann Rupert da Nicky Oppenheimer, da kuma ɗan masar Nassef Sawiris da sauransu , manyan attajirai suna ci gaba da gina dauloli na kamfanoni.
Haƙiƙa ta duniya
Amma wannan ba batun da ya shafi Afirka ba ne kawai. Haƙiƙa ce ta duniya . Rahoton rashin daidaito na shekarar 2026 na gidauniyar binciken rashin daidaito da Majalisar Ɗinkin Duniya ta mara wa baya ta ce har yanzu akwai bambanci “mai yawa da ya ƙi tafiya” a fadin duniya.
Rahoton ya ce “kashi 10 cikin 100 na masu samun kuɗin shiga a duniya suna samun abin da ya fi samun saura kashi 90 cikin 100.”
Amma me ya sa hakan?
Rahoton rashin daidaito na duniya ya ce abin da ke tunzura matsalar shi ne tsari mai rauni na karɓar haraji daga attajirai da taruwar jari a wurare kaɗan sosai da kuma rashin daidaito na damar samun ilimi da damarmaki.
Wasu daga cikin waɗanda ke da arzikin sosai ma suna amfani da “tasirin siyasa ” wajen juya gwamnati. Wannan na sa attajirai su hana sauye-sauyen da za su iya amfanar talakawa, domin kare harkokin kasuwancinsu.
Harkokin kasuwancinsu ma su suke samar da hayaƙi mai gurɓata yanayi da ya fi shafar talakawa.
Fiye da mutum miliyan 460 a Afirka suna rayuwa cikin ‘matsanancin talauci’ a shekarar 2025. Bankin duniya ne ya yi wannan bayanin .
Tsare-tsaren kuɗi
Ƙwararru sun ce talauci ba rashin kuɗi ba ne a cikin al’umma. Akwai kudi masu yawa . Ƙalubalen shi ne yadda suke gudana. Wasu daga cikin masu kuɗi suna samar da ayyukan yi , suna ba da gudumowa kuma suna ba da kudi domin tafiyar da harkar ilimi da ta lafiya.
Amman masu bincike sun ce tsare-tsaren kuɗi na duniya suna da matsala, inda suke bari manyan attajirai ke tara kuɗaɗe cikin sauƙi. Wannan rashin daidaiton na buƙatar a magance shi. Rahoton rashi daidaito ya jaddada cewa wannan ba batun ba da taimako a hannu ba ne kawai.
Dole a samu damar samun ilimi ga kowa a duniya gabaɗaya – babu bambanci tsakanin ‘ya’yan masu kudi da na marasa galihu.
Ya kuma goyi bayan kawo ƙarshen tsarin haraji da ya fi taimaka wa masu kuɗi, da kuma zuba jari da yawa a cikin gida domin samar da ƙarin ayyukan yi, yayin da gwamnatoci suke aiwatar da manufofi na tattalin arziki masu taimaka wa da yawan mutane da kuma yaƙar cin ganci da rashawa.
















