Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis

Yayin da wasu ƙasashe ke dogara ga ganin watan Ramadan a yankunansu, wasu kuma suna amfani da lissafin ilmin taurari don tantance farkon watan, musamman lokacin da bayanan kimiyya suka tabbatar da rashin ganin watan da ido kadai.

By
Musulmai a Türkiye, Oman, Singapore, da Ostiraliya za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis. / AP

Musulmai a ƙasashen Turkiyya, Oman, Singapore da kuma Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis, bayan da hukumomi a kasashe hudu suka tabbatar da fara watan Ramadan bisa ga lissafin ilmin taurari.

Safi Arpagus, shugaban Hukumar Kula da Addini ta Turkiyya, ya ce za a yi Tarawih na farko (addu'o'i na musamman na dare a lokacin Ramadan) a ranar Laraba kuma daren farko na azumi da zai kasance ranar Alhamis.

Kazalika Oman ita ma ta tabbatar da cewa Musulmai a ƙasar za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis.

Hukumomi a ƙasar sun ce ranar Laraba za ta zama ranar ƙarshe a Shaaban, wato wata na takwas a kalandar Musulunci, ba tare da ta buƙaci al’umma su yi dubar wata ba.

Mataimakin Babban Mufti na ƙasar Kahlan bin Nabhan al-Kharousi ya ce shawarar ta dogara ne da ka'idojin addini da kimiyya da aka dade ana amfani da su.

Musulmai a Singapore za suma za su fara azumin watan Ramadan a ranar 19 ga Fabrairu, a cewar wata sanarwa da Majalisar Addinin Musulunci ta Singapore (Muis) ta fitar.

Mufti Nazirudin Mohd Nasir ya ce lissafin ilmin taurari ya nuna cewa ba za a ga sabon watan Ramadan ba da kuma faɗuwar rana a ranar 17 ga Fabrairu, ma'ana ranar ƙarshe ta Sha’aban za ta kasance 18 ga Fabrairun 2026 kuma farkon ranar Ramadan za ta kasance ranar 19 ga Fabrairu.

Australia ta kuma tabbatar da cewa watan azumi zai kankama a ranar Alhamis, bisa ga lissafin ilmin taurari, bisa ga lissafin da Majalisar Fatawa ta Australia ta amince da shi bayan shawarwari da aka gabatar wanda Babban Mufti Ibrahim Abu Mohamad ya jagoranta.

Ramadan shine wata na tara a kalandar Musulunci kuma ana soma azumi a watan da zarar an ga wata.

Yayin da wasu ƙasashe ke dogara ga ganin watan Ramadan a yankunansu, wasu kuma suna amfani da lissafin ilmin taurari don tantance farkon watan, musamman lokacin da bayanan kimiyya suka tabbatar da rashin ganin watan da ido kadai.